Connect with us

LABARAI

Gwamna El-Rufai Ya Gagauta Korarar Masu Bashi Shawara –Na Tatu

Published

on


Dan takarar Majisar Dokoki ta jahar Kaduna a karkahin jam’iyar sa ta APC Sanusi Aminu Shu’abu Sani Na Tatu, ya yi kira ga Gwamnan jahar Malam Nasir Ahmed el-rufai da ya gaggauta sauke daukacin masu bashi shawara da suke son tsayawa takara a kakar zaben shekarar 2019.
Na Tatu wanda yake son ya wakilci alummar sa na mazabar anguwar Sanusi ya yi kiran ne a hirar sa da LEADERSHIP Hausa Ayau a Kaduna.
Acewar sa, tsakani ga Allah baza ta sabu ba ace masu baiwa gwamnan shawarar da suke son yi takara a shekarar 2019 kuma suci gaba da zama akan madafun su na iko har zuwa yanzu ba.
Na Tatu ya yi nuni da cewar, babu wata shawara kirki da masu bayar da shawarar za su iya yi a wannan dan gajeren lokacin da zaben 2019 ke kara kunno kai, sai dai, za su fi mayar da hankulan su ne akan takarar su mai makon baiwa gwamnan kyawawan shawarwari da sai sake lashe zabe karo na biyu da kuma yiwa APC aiki tukuru.
Da yake tsokaci akan takarar sa, Na Tatu yace, “alummar mazabar sa musamman ‘yan uwana nakasassu ne suka ga ya dace in fito don in wakilce ganin irin tallafin dana ke bayar wa wajen inganta rayuwar alumma musaman ma su nakasassun.”
Ya yi nuni da cewar ba wani aibi bane don nakasasshe ya fito takara ba domin a wasu sassan kasar nan, an zabi irin su a madafun iko wasu kuma an nada su a mukamai a matakai da ban-da-ban domin an san akwai gudunmamawar da za su iya bayarwa wajen ciyar da tattalin arzikin kasa da kuma dimokiradiyya.
Na Tatu ya kara da cewar,’ in har alummar mazabar sa suka bashi damar wakilci, zai tabbatar da ya gabatar da kodurori da za su ciyar da jahar da kuma mazabar.
Acewar,” zanyi iya kokari na, musamman wajen mayar da hankali akan gabatar da kodurorin da za su inganta rayuwar nakasassu ‘yan uwana dake aukacin jihar.”
A karshe, Na Tatu ya yi kira ga daukacin alummar jahar dasu sake bai wa gwamnan jahar goyon baya don kamma ayyukan ci gaba da faro.


Advertisement
Click to comment

labarai