Connect with us

LABARAI

Buhari Zai Je Bauchi Domin Jajen Ibtila’in Guguwa –Gwamna Abubakar

Published

on


Gwamnan Jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar ya shaida cewar suna sa ran shugaban Nijeriya Muhammad Buhari zai kai wata ziyara ta musamman domin jajanta wa jama’an jihar Bauchi a bisa ibtila’in Guguwa mai karfin gaske wacce ta auku a ranar Asabar din da ta gabata a jihar hade da jajanta ibtila’in Gobara wacce ta cinye kasuwar Azare da ke karamar hukumar Katagum.
Bayanin hakan ya fito ne daga fadar jihar Bauchi a cikin sanarwar da sakataren watsa labarai na gwamnan jihar Bauchi, Abubakar Al-Sadikue ya sanya wa hanu hade da aike wa ‘yan jarida, ya ci gaba da cewa, gwamnan jihar ta Bauchi ya shaida cewar, sun tattauna da shugaban kasar inda ya bayyana masa irin barnar da Guguwar ta yi a jihar ta Bauchi.
Sanarwar ta ce; “Mun yi magana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin kan wannan musifar da suka auku mana a jere a jihar. ya mika jajensa ga illahirin jama’an jihar Bauchi, haka kuma ya jajanta wa gwamna da sarkin Bauchi kan lamarin,” In ji Abubukar.
Gwamnan kamar yadda sanawar ta shaida, ya gode wa shugaban kasan kan nuna gayar damuwarsa kan ibtila’in da ta auku a jihar ta Bauchi, ya nemi illahirin jama’an jihar Bauchi da su fito kansu da kwarkwatansu su marabci shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin da ya kawo ziyara domin jajantawa da kuma ganin irin barnar da ta auku a jihar.
Abubakar Al-Sadikue ya kuma shaida cewar gwamnan jihar ya tashi tsaye domin ganin an samar da kayyakin rage radadi wa wadanda ibtila’in ta shafa, inda yake cewa “A sakamakon Guguwar da aka yi a jihar Bauchi ranar Asabar, gwamnan jihar ya raba kayyakin jinkai wa jama’an da abun ya shafa domin su samu nasarar sake gina muhallansu da suka lalace kan wannan matsalar,” In ji Sanarwar.


Advertisement
Click to comment

labarai