Connect with us

LABARAI

An Bukaci Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kawo Wa Kasuwar Sheme Dauki

Published

on


Shugaban kungiyar Sarakunan shanun zango da dillalai na jihar Katsina, Sarkin Shanun Faskari na 2 Alh. Aminu Umar Sheme. ya yi kira ga Gwamatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari da ya dubi kasuwar shanun sheme cikin aiyukan alheri da yake shimfidawa a jihar ta Katsina.
Sarkin shanun ya ce, an gina kasuwar ne fiye da shekara 40 da suka shude, domin amfanar manoma da makiyaya da falake da ke fadinAarewacin kasar nan kai harma da kudancin kasar nan baki daya, Mutane ke tururuwa zuwa kasuwar ta Sheme duk ranar Juma’a domin safarar dabbobin, Amman abin bakin ciki da damuwa katangun kasuwar suna neman su zube in ba a dauki matakin gyara ba, domin raban kasuwar da ta samu gyara tun lokacin marigayi Umaru Musa Yar aduwa na gwamna a zangon mulkinsa na farko, inda shugaban karamar Hukumar Faskari Alhaji Saidu Umar Mami ya fadada kasuwar a shekarar 1999,
Don haka suke kira ga Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari, daya taimaka ya kula da kasuwar, wace duk kudancin Katsina ba kasuwar shanu kamarta. Wanda tana da manya da matsakaita dillalai, Allah kadai ya san mutanen dake cin abinci a kasuwar,
Kuma gyara wurin zai magance satar dabbobi yayin da aka tafi sallar Juma’a.


Advertisement
Click to comment

labarai