Connect with us

LABARAI

Rundunar ’Yan Sanda Ta Kori Kwamandan Rundunarta Mai Yaki Da Kungiyoyin Asiri

Published

on


Koke-koken yawaitar cin hanci da karban rashawa da kuma nuna halayya mara kyau, sun tilasta Jihar Legas koran kwamandan sashen ta na masu yaki da ‘yan kungiyar asiri.
Rundunar kuma ta canza wa wasu jami’anta na sashen nata na musamman wuraren aiki.
Cikin wata sanarwa wacce Kakakin rundunar, Mista Chike Oti, ya fitar, ya ce, jami’in da ke kula da sashen, Mista Godwin Agbegbe, an cire shi ne musamman saboda zargin rashin iya tafiyar da aiki da kuma cin hanci da karban rashawa.
Mafiya yawan jami’an ‘yan sandan da suka yi aiki a karkashinsa duk an ce su koma shalkwatar rundunar domin a canza masu wuraren aiki.
Shi kuma an canza shi da Mista Akaninyene Etuk.
Oti ya ce, Kwamishinan ‘yan sandan na Jihar, Mista Imohimi Edgal, ya nemi hadin kan al’ummar Jihar kan yakin da rundunar ke yi da aikata laifuka da kuma ayyukan kungiyoyin asiri.
Ya bukaci al’umma da su rika taimaka wa rundunar da bayanai masu mahimmanci kan ayyukan kungiyoyin sirrin a kowane sashe na Jihar ta hanyar tuntubar kwamandan sashen kai tsaye a lambar wayarsa mai lamba, 08034448617.
Ya kuma bayar da tabbacin boye sirrin duk wanda ya tona asirin wasu batagari a Jihar.
Sai dai kuma, an sami rahoton gabza wani mummunan fada a tsakanin wasu kungiyoyin asiri biyu masu gaba da juna wanda har ya yi sanadiyyar mutuwar daya daga cikinsu a Unguwar Alapere, da ke Yankin Ketu, kusa da Legas.
Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ya ce, fadan ya faru ne a wani waje da ke kan titin Modupe, daura da layin Kazeem, da ke Alapere, da daren ranar 17 ga watan Yuni.
Wani mazaunin Unguwar wanda ya shaidi fadan, ya ce, ‘yan kungiyar asirin sun zo ne daga wani layin da ke kusa da wannan, wanda a cewarsa, layin matattaran ‘yan kungiyar ne.
Wata majiyar da ba ta so a ambaci sunanta ba, ta bayyana sunan kungiyoyin asirin da, Eiye da kuma Aye.
“Sun jima kullum suna fada da junansu, a duk dare sai su kwana suna harbi da bindigogi.
“Kazeem, Aminu da layin Akampson kusa da injin bayar da hasken lantarki da ke Alapere, wurare ne masu hadari domin ayyukan ‘yan kungiyoyin asirin,” in ji shi.
Oti, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce, wanda ya mutun da wuka ne aka soke shi.
Ya kuma ce, har yanzun ba a iya gano asalin wanda aka kashen ba.
Amma ya ce, kawo yanzun dai ba su iya kama kowa ba.


Advertisement
Click to comment

labarai