Connect with us

LABARAI

Guguwa: Turakun Wutar Lantarki 300 Ne Suka Karye A Bauchi, Inji JED

Published

on


Sama da turakun wutar lantarki wato fol-fol guda xari uku 300 ne suka karya gami da lalacewa a cikin kwaryar jihar Bauchi a sakamakon mummunar Guguwar da aka yi a jihar Bauchi a ranar Asabar.
Daraktan da ke kula da shiyyar Bauchi a kamfanin rarraba wutar lantarki ta Jos Electricity Distribution Company (JED), Alhaji Hafis Saleh Hassan shine ya shaida hakan zantawarsa da manema labaru a Bauchi dangane da yanayin barnar da Guguwar ta yi wa turakan wutar lantarkin.
Daraktan ya bayyana cewar baya ga fol-fol xin da Guguwar ta karya musu guda 300, ta kuma barnata wayoyin wuta da sauran kayyakin wutar lantarki da daman gaske a cikin jihar ta Bauchi.
A lokacin da ke zagawa da ‘yan jarida domin gani da ido irin barnar da Guguwar ta yi wa jama’an jihar ta Bauchi, shugaban sashin ‘Head of Technical Unit’, reshen jihar Bauchi Injiniya Abdullahi Hussain ya ce, kawo yanzu suna kan ci gaba da tattara bayanai yanayin ababen da suka yi asarar domin aikewa da shi ya zuwa babban ofishinsu da ke Jos domin xaukan matakin gyarawa domin daidaito da wutar a cikin jihar.
Shugaban ya kuma jawo hankalin gwamnatoci da kuma sarauka, limamai da sauran masu faxa a ji da su yi kokarin bayar da kariya wa kayyakin wutar da suke yankunansu domin kauce wa masu barnatawa.
Da yake mika sakonsa ga illahiran jama’an jihar garin Bauchi, Alhaji Hafis Saleh Hassan ya baiwa jama’an cikin garin Bauchi hakuri, inda yake shaida musu cewar kawo yanzu wutar lantarki a jihar zai xauki xan wani lokaci gabanin a kawo musu, yana mai shaida cewar sai sun samu nasarar kammala dukkanin gyare-gyare gabanin su sake wutar wa jama’a domin kare musu lafiyarsu.
Abdullahi ya kuma shaida cewar za kuma su tsunduma zuwa sauran kananan hukumomin jihar ta Bauchi da Guguwar ta barnata domin tattaro yanayin asarar da aka samu a sashin wutar lantarkin, domin xaukan matakan gyarawa.
Ya ce; “Kamfaninmu tana kan gudanar da aiki domin tabbatar da dawowar wuta a cikin Bauchi. Don haka, mazauna cikin garin na Bauchi su kasance masu hakuri har zuwa lokacin da za mu samu nasarar shawo kan matsalar, muna kuma shawartar gwamnatin jihar ta taimaka musu,” Inji Injiniya Abdullahi.
Ita dai wannan Guguwar wacce ta auku a ranar Asabar ta janyo asaran ababe da daman gaske, lamarin da ke nuni da cewar babu wani wajen da barnar bai shafa ba a cikin jihar ta Bauchi.


Advertisement
Click to comment

labarai