Connect with us

LABARAI

Burina Ciyar Da Matasa Gaba –Jabiru Kilawa

Published

on


Wani matashin dan siyasa a jihar Gombe mai neman kujerar majalisar tsara dokokin jihar a yankin Gombe ta kudu a jam’iyyar APC Alhaji Jabiru Saleh Kilawa Zanna, ya ce siyasar sa ta ciyar da matasa gaba ne da samar musu da hanyoyin dogaro da kai idan yaci zabe.
Jabiru Saleh Kilawa, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da LEADERSHIP A Yau a Gombe inda ya ce yana da kyau matasa da sauran al’umma su dinga sanin irin mutanen da za su zaba dan zame musu shugabanin da za su wakilce su saboda yanzu lokaci ya canja da mutane za su tura mota ta tashi ta bar su da kura.
Ya ce shi ba zai yi siyasar banga ba irin yadda wasu ke tara matasa suna basu makamai da kayan maye ba shi a cewar sa abunda yasa ya shiga ma siyasa shi ne a har kullum rokon Allah yake ya ba shi daman da zai zama shugaba dan ya kawo gyara a irin siyasar da aka jima ana yi na ta’addanci.
Zanna ya kuma kara da cewa bayan ya samarwa da matasa aikin yi zai yi kokari yaga mazabar sa wato Gombe ta kudu ta kunshi unguwanin Bolari ta gabas da Bolari ta yamma da Kumbiya-Kumbiya da Pantami da Jekadafari sun shaida ribar mulkin siyasa a ta dalilin sa.
A cewar sa yana kuma so ya hada kai da gwamnati dan in sha Allah a shekarar 2019 APC ce za ta kafa gwamnati a jihar idan ya zama zababben dan majalisa zai yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin cewa al’ummar jihar ba na mazabar sa kadai ba sun gane cewa an samu canjin gwamnati domin zai hada kai da sauran yan majalisun suna bai wa gwamna shawarin da zai taimaki al’ummar jihar Gombe.
Jabiru Saleh Kilawa, ya yi amfani da wannan damar ya bai wa ‘ya’yan jam’iyyar su ta APC shawarar cewa su hada su ceto jihar Gombe domin idan basu hada kai ba babu yadda za’a burin su ya cika, sai kuma ya sake yin kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da cewa su bai wa jagororin jam’iyyar hadin kai wajen babban taron su da zai gudana a ranar asabar mai zuwa a babban birnin tarayyar Najeriya dan a samu taron ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Sannan ya kuma ce ba yadda za’ayi su canja gwamnati sai sun hada kai sannan kuma sai kowa ya yanki katin zabe domin duk yadda kake son mutum idan baka da katin zabe ba za ka iya zabar sa ba.
Daga nan sai ya ce a gwada a gani tana maganin mai gardama dan haka jama’ar Gombe ta kudu su gwada shi su ga yadda zai tabbatarwa da matasa mafarkin sa a 2019.


Advertisement
Click to comment

labarai