Connect with us

LABARAI

NAFDAC Ta Bukaci A Tsananta Horo A Kan Masu Yin Magungunan Bogi

Published

on


Hukumar NAFDAC ta nemi a samar da horo mai tsanani ga masu yin magungunan jabu a kasar nan don ya zama darasi ga sauran yan Nijeriya.
Shugaban hukumar NAFDAC, Farfeaa Moji Adeyeye, ce ta yi wannan kiran a garin Abuja a wata tattaunawarta dabyan jarida.l ranar Litinin.
Adeyeye ta lura da cewa, dokoki da horon masu laifufukan da suka shafi sarrafa kwayoyi da magunguna sun tanadi horo masu rauni, saboda haka ta bukaci sake fasalin dokokin.
Ta ce, hukumar ta mika wa majalisar kasa sabon doka inda take neman tsatsauran horo ga wadanda suke yin jabun magunguna.
“Jabun magunguna na kashe mutane amma horon da ake bai wa masu yin jabun magungunan bashi da wani tasiri in aka kwatanta da girman laifin”
“Hukuncin watanni ko shekara biyu a gidan yari bai isa ba.
“Dole mu samar da doka mai tsauri da zai tanadi horo mai tsanani ga masu yin magunhunan jabu” inji ta.
Shugaban hukumar ta kuma lura cewa, lamarin abinci da magunguna nada matukar mahimmamcin da bai kamata a yi wasa dasu ba.
Ta kuma yi alkawarin cewa, hukumar zata tabbatarbda dukkan masu hulda da kuma yin jabun magunguna sun dandana kudarsu.
Adeyeye ta ce, a halin yanzu hukumar sake sabbin tsare tsare don ganin an kare rayuwar mutanen kasa baki daya.


Advertisement
Click to comment

labarai