Connect with us

RA'AYI

Tsakanin Baba Da Babawo!

Published

on


Dukkansu sun haura shekaru 70 a duniya, babu ’yan kishin kasa (Nationalists) kamarsu, domin sun sadaukar da rayukansu a fagen daga domin tabbatar da dorewar Najeriya a matsayin kasa dunkulalliya gudadaya. Sannan kowannensu ya kai kokoluwar makami a matsayin hafsoshin soja, kuma sun yi mulki karo biyu, wato a kaki tare da cin zabe a tsarin dimukradiyya. Baba (Buhari) da Babawo (Obasanjo) sun kasance turaku a cikin tarihin kasarmu Najeriya. Amma abubuwa da dama sun bambanta wadannan jarumai namu. Na farko dai a tsawon mukaman da su ka rike ba a taba samun zargi na cin hanci, rashawa ko sama da fabi ba daga wajen Baba Buhari ba, amma shi kuwa Babawo Obasanjo ya kasance cikin zarge-zarge iri-iri. Na farko bayan ya sauka daga mulkin soja a shekarar 1979, inda ya kafa tarihi na mika mulki a hannun farar hula, sai ga shi ya gina makekiyar gona a garinsu ta Ota wadda babu irinta a duk fadin yankin Yammacin Afrika (a ina ya samu wannan kudi?).

Babawo ya sami daukaka bayan ajiye mulki saboda tarihin da ya kafa yadda a shekarun 1980 an yi ta kamfen don a ba shi babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, wanda Babangida ya yi masa makarkashiya, ina ganin kuma abinda ya sa gabarsu ta yi tsamari kenan. A shekarar 1999, a kokarinsa na wanke kansa daga gabar da ke tsakaninsu da kuma neman dawo da kimarsa a wajen Yarabawa, Babangida ya sa an fito da Babawo daga kurkuku su ka ba shi takara a PDP, inda su ka taimaka ma sa ya lashe zaben. Fitowarsa daga kurkuku an ce Naira 20,000 kacal ke cikin asusun ajiyarsa, amma a wannan shekara ta 2018 shafin nigerianinfopedia ya kiyasta arzikin Babawo a matsayin Dala biliyan 1.8, wato kimanin Naira biliyan 648, fiye da rabin Tiriliyon kenan (Ina ganin jarin 20,000 din nan ne a Ota ya kawo wannan riba ko?).

Babawo ya kafa tarihi a karo na biyu wajen dare wa mulkin Najeriya a matsayin farar hula, kuma ya kawo abubuwa masu mahimmancin gaske a tsarin cigaban kasa, musamman jawo zakakuran matasa masu ilimi cikin gwamnatinsa da kafa hukumar EFCC. Sai dai gazawarsa wajen gina ginshikai na cigaba irinsu tabbatar da yaki da rashawa ba-sani-ba-sabo da kuma dabbaka ginshikan siyasa, abinda ya ja gwamnatinsa ta kasa kai gaci kenan. Babawo ya lalata tsarin dimukradiyya wajen tilasta ra’ayinsa ga ’yan siyasa ta hanyar barazana ko ba su na goro. Mun ga yadda a ka dinga canza shugabannin majalisar dattawa kamar cire hula a mulkinsa, mun ga kuma yadda a ka dinga kawo buhunan bakko cike da Nairori don bawa ’yan majalisa cin hanci. Mun ga yadda a ka dinga fafarar gwamnoni tare da tsige su, don sun ki ba shi goyon baya.

Zunubi mafi girma da Obasanjo ya aikata shi ne na kokarin yin tazarce; abinda ya yi yaki da shi a lokacin Sani Abacha, wanda hakan ya kai shi ga kurkuku. Sanatoci da dama sun bayyana yadda su ka karba ko su ka ki karbar cin hancin Naira miliyan 50, don kada kuri’ar ya zarce. Wadannan abubuwa sun gurgunta jaririyar dimukradiyyar Najeriya sannan su ka bawa cin hanci da rashawa gindin zama a siyasarmu.

Babawo ya fusata sosai wajen hana shi tazarce, kuma da ya ke shi mutum ne maras yafiya, kamar yadda ’yarsa ta cikinsa, Iyabo, ta fada wa duniya, ya dauki kudirin ramuwa a kan duk ’yan Najeriya. Mutane da dama na raina Obasanjo saboda siffarsa ta dolaye, amma a bayan wannan fuska mutum ne mai tsananin kaifin basira da iya lissafi, kamar yadda Malam Nasir El-Rufai ya fada cikin littafinsa na “Accidental Public Serbant” cewa Obasanjo ya ce ma sa Nasiru dole ka rika samun matsala da mutane, domin da an gan ka an san mutum ne kai mai basira, amma ni a kan raina ni, wanda hakan ya ke ba ni damar yin nasara a kan mutane.

Domin azabtar da ’yan Najeriya saboda kin ba shi goyon bayan tazarce sai ya lalubo mutane biyu domin su gaje shi; Yar’Adua da Jonathan. Yar’Adua kowa ya san ba shi da lafiya, wasu likitoci ma na cewa ba zai shekara ba. Jonathan dan Niger-Delta ne kuma matashi wanda bai goge da rikita-rikitar siyasar Najeriya ba. Kowa zai iya mulkin Najeriya daga manyan kabilun da a ke da su, amma banda dan Niger-Delta, saboda mutane ne da ba su san komai ba sai kudi. A tarihi mun ga yadda su ka kasance kabilar da ta fi bawa Turawa wahala, saboda kasancewar ba su da tsarin zamantakewa a dunkule irin yadda Yarabawa da Hausawa ke da shi, sannan da son biyan bukatarsu kawai. Ba sai na koma kan yadda Yar’Adua ya mutu kuma Jonathan ya kusa rushe Najeriya ba.

Shi kansa Baba, kasancewarsa dan kishin kasa kamar yadda na fada a baya (Nationalists), ya yi danasanin bulalar da ya yi wa ’yan Najeriya. Don haka ya yi maza-maza ya juya wa gwamnatin Jonathan baya kuma ya bada gudunmuwa wajen kayar da ita a zaben 2015. Babawo da bakinsa ya fada cikin littafinsa na baya-bayan nan, wato ‘My watch’ cewa da ya zabi Jonathan gara ya zabi Buhari ko da kuwa Buhari zai daure shi. Abin tambaya a nan jama’a shi ne, idan babu rami me ya kawo rami? Babawo ya goyi bayan Baba ne domin ya san babu wanda zai iya ceto Najeriya a wannan gaba idan ba shi ba, amma kuma Ina zaton ya yi tsammanin cewa Buhari zai zama irin Yar’Adua ne; ba zai iya karasa zangon farko na mulkinsa ba.

Bayan Baba Buhari ya dawo daga jiyya kuma ya dawo da karfinsa sannan kuma ya nuna sha’awarsa ta neman takara a karo na biyu, nan ne fa hankalin maza ya tashi. Duk yadda za su yi su hana shi zarcewa sai sun yi, don haka Babawo ya fitar da wasikarsa ya na kiran Buhari ya hakura, sannan dan uwansa na Minna shi ma ya goya ma sa baya. Shin Babawo ya manta cewa bayan wa’adin mulki karo biyu sai da ya yi kokarin tazarce? Wanda ya yi wannan har ya na da bakin kiran wani kada ya nemi wa’adi na biyu halartacce?

Tun zamanin Awolowo ba a sake samun shugaba da Yarabawa su ka yi na’am da shi irin Baba Buhari ba, kuma duk da kasancewar Babawo Bayarabe ne bai taba samun karbuwa irin wadda Baba ya ke da ita yanzu a kasar Yarabawa ba. Su Babawo sun kwana da sanin cewa matukar Baba ya zarce a karo na biyu sai ya rufe tarihinsu kakaf a siyasar Najeriya, don haka za su yi duk yadda za su yi wajen ganin sun tankwabe wannan dama.

Don haka mu na kira ga Baba, lallai ne ya jajirce wajen ganin ya sa an kakkabe duk wasu zarge-zarge da EFCC a karkashin Ibrahim Lamurde ta wanke Babawo, wajibi a bude sabon bincike, don nemo ma na yadda a ka kashe wadannan makudan kudade ba tare da samun wutar lantarki ba. Tsohon Kakakin majalisar wakilai ta kasa, Dimeji Bankole, ya tabbatar da cewa an ware da kuma sahale kashe Dala biliyan 16 tsakankanin shekarun 1999 zuwa 2007 a karkashin mulkin Obasanjo kuma a ciki ya tabbatar da cewa an fitar da tsabar kudi Dala biliyan 13.5, kimanin Naira Tiriliyan shida kenan.

Wadannan kudade mun ga yadda a kasashe irinsu South Korea, Saudi Arabia, U.S.A, Taiwan, Hong Kong, Medico da Chile su ka samar da wutar da ta kai kimanin Mega Watt 6000. Ba za mu manta cewa a lokacin da Baba ya shigo gwamnati a shekarar 2015 wutar lantarkin Najeriya sai da ta yi kasa zuwa Mega Watt 1000 kacal ba, amma yanzu gwamnatin ka na iya samar da kimanin Mega Watt 7000 ba tare da kashe wasu makudai ba.

Wani sauti na bayani da Marigayi Albani na Zaria ya saki ya yi ikirarin cewa Bola Ige ya ce Shugaba Obasanjo ya nemi da a saka wasu makudan kudade da gwamnatinsa ta ware don gyaran NEPA a cikin asusun ajiyarsa wanda shi Bola Igen ya ki yarda da hakan, kuma sakamakon haka a ka je har gida a ka kashe shi. Sannan Albani ya kara da cewa a lokacin Yar’Adua shi da kansa ya yi silar da gwamnatin Saudiyya ta bawa Najeriya injina da kayan aiki da su ka hada har da wayoyin lantarki da falafalai na biliyoyin Nairori kuma Mangal da Dr Aliyu Abdullahi Damau, wato babban sakatare na ma’aikatar makamashi, ne su ka je har Saudiyya su ka karbo wadannan kayayyaki. Bayan sun dawo kuma Yar’Adua ya ware Naira biliyan 11 domin aikin, amma babu kudin babu kayan aikin.

Don haka Ya Shugaba a gaggauta kafa mai bincike na musamman mai zaman kansa, domin mun ga yadda majalisa ta yi walakolombo da binciken a baya, kuma EFCC ma makiyanka za su ce karen faruta ce, amma mai bincike mai zaman kansa ya na da damar bincikar rahoton da Ndudi Elumelu ya gabatar wa majalisa a 2009. Sannan a gayyato mutane irinsu Obasanjo, Lyel Imoke, Segun Agagu, Abdulhamid Ahmed, Joseph Makoju, G.O.P. Osakue, C.E. Ifesie, Mike Ezeudenna, C.N. Nwachukwu, I. Onuoha da J. A. Olotu, Mangal da Aliyu Damau har da CBN da sauran duk wadanda ke da wata masaniya game da harkar wutar lantarki tun daga shekarar 1999 tare da duk kamfanonin da a ka ba su kwangiloli karkashin tsarin NIPP lokacin mulkin Obasanjo.

Haka ne kadai zai sa mu san cewa ko tsohon Shugaba Obasanjo na da hannu ciki badakala mafi girma a tarihin cin hanci da rashawa na wannan kasa tamu ko kuwa a’a!

 


Advertisement
Click to comment

labarai