Connect with us

DAUSAYIN MUSULUNCI

Ramadan; Babbar Makaranta Ga Muminai!!!

Published

on


Yan’uwana Musulmai! Farin ciki mai yawa yana nan a lokacin da muka riski watan Ramadan, a yau kuma muna nan tsakanin tsoro da fata. Harsuna suna masu furuci da addu’a akan Allah ya karba mana azuminmu da tsayuwarmu, fatanmu Allah ya karba mana abin da ya shude, Ya sanya albarka cikin abin da zai zo nan gaba. Hakika jin dadi da rabauta ya tabbata ga wadanda aka gafarta musu! Jin dadi ya tabbata ga wadanda aka karbi tubansu. A karshen wannan wata, muna godewa Allah da ya ba mu damar yin bautarSa da dace da muka yi na tsayuwa da azumtar wannan wata, da sauran harkoki na ibada.

Yan’uwana Musulmai! Neman gafara a gurin Allah shi ne cikamakon aiyuka nagari, da shi ake rufe sallah, da shi ake rufe aikin Hajji, da shi ake rufe majalisu. Don haka ya zama wajibi a rufe azumi da shi, ba don komai ba sai don mu mikar da abin da ya samu tankwasa cikin azuminmu. Lalle istigfari, yakan kankare duk abin da ya fadawa zuciya na girman kai da sabon Allah.

Yan’uwana Musulmai! Duk wata da’a da mutum zai yi, ba ta da kima ko wata daraja idan har mutum bai ji tana da tasiri na tsoron Allah a tattare da shi ba. Ina alama na cewar ka yi azumi alhali bayan Ramadan ka kauracewa Alkur’ani! Ka bar sallah cikin jama’a! Ka kutsa cikin haramtattun abubuwa! Ina alama ta cewa ka bautawa Allah, alhali Ramadan na shudewa ka koma cin kudin ruwa da dukiyar mutane bisa zalunci! Ina alamar cewa ka yi azumi, alhali ka bar Sunna ka koma kutsawa cikin muggan al’adu da bidi’o’i! Ina alamar cewa ka yi azumi a matsayinka na dan kasuwa, ka koma kana cin dukiyar mutane da wayo da rantsuwar karya! Ina alamar cewa ka yi Kiyamul Laili, alhali wata na shudewa ba ka yi wa wanda ke cikin bata nasiha ba, ko ciyar da wanda ke cikin halin yunwa, ko tufatar da wanda ke cikin halin tsiraici! Ina alamar cewa ka yi da’a a watan Ramadan ana hada baki da kai ana danne hakkokin al’umma da cutar da su da tauye musu hakkoki nasu! Ina alamar cewa ka yi azumi amma kana zaluntar al’umma cikin mutuncinsu da dukiyoyinsu da kokarin shiga tsakaninsu da aiyukansu da barazana da rayuwarsu.

Yan’uwana Musulmai! Ba motsin gangar jikinmu kawai Allah ke bukata ba, a’a akwai wasu abubuwa wanda kan gaba su ne tsoron Allah. Lalle Allah yana cewa “…….an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka gabacewa ku, fata ku yi takawa”.

Yan’uwana musulmi! Hakika al’ummar musulmi sun azumci watan Ramadan, sun yi aiyuka na ibadu cikinsa, sun ciyar da mayunwata, sun tufatar da matsiraita. Sai dai ba a karbi ba a karbi ciyarwarsu, da tufatarwarsu ba, ba don komai ba, sai domin ba su nufaci Allah cikin aiyukansu ba, rashin iklasi ya musu katanga tsakaninsu da niyyoyinsu. Wasu kuwa an karbi dukkanin ibadunsu, ciyarwarsu, tufatarwarsu, ba domin kyawun shigarsu ba, ko domin kyawaun jikinsu, ko kuma domin iya tsara lafuzansu wajen magana, an karbi aiyukansu domin iklasi ya dabaibaye su. Madallah da wadanda aka karbi aiyukansu, tir da kaico ga wadanda aka yi watsi da aiyukansu.

Yan’uwana musulmi! Ramadan ya tafi a daidai lokacin da ma’abota tsoron Allah suka zub-da-hawaye, suka yi kuka na takaici, ba don sun rabu da gasar ciye-ciye da tande-tande ba, sai domin rashin tabbas na sake riskar wannan wata a wadansu shekaru masu zuwa, ko domin rashin samun nutsuwa na bautar Allah. Sai dai tafiyar watan Ramadan ba ya nufin dakatawar aiyukan alheri, ba ya nufin daina tsayuwar dare, ko yin azumi, ko tufatar da matsiraita, ko ciyar da mayunwata. Lalle watan Ramadan ya dasa mana alherai, ya karantar da mu darusa, ya wanke mana kwakwale, ya farkar da mu, ya tsarkake mana zukata. Wanda ya yi amfani da wannan wata za ka same shi a bayansa yana mai ci gaba da irin abubuwan da ya koyo. Wanda ya juya baya kuwa, ba abin da ke tattare da face tabewa da asara.

Yan’uwana Musulmai! Lalle abin lura ga wannan rayuwa, abin da yakamata mu hankalta da shi, abin da zai zame mana izna da wa’azi, shi ne gaggawa wajen shudewar zamuna. Kamar ba jiya muka zauna muna dakon jiran watan Ramadan ba! Kamar ba yau muka fara azumtarsa ba! Amma kash! Ramadan ya wuce sai dai tarihi, ya tattara dukkanin aiyukan da bayi suka aikata ya tafi da shi, za ya kasance mai shaida akan mu, ko a gare mu. Lalle shudewar zamuna cikin gaggawa abaiban tsoro ne ga mai hankali, abaibai wa’azi ne ga masu tunani da muminai. Kenan ya zama wajibi kowannenmu ya fadaku, ya gyara aiyukansa, ya tuba daga zunubansa, ya koma ga Allah; komawa ta hakika ta tabbas, ya sani rayuwar duniyar nan ba komai ba ce face rudi na shaidan da hayaniya, wanda ya fahimci haka, za ka same shi yana taka-tsantsan cikin lamuransa na duniya, da kuma nutsuwa da gamsuwa cikin ibadunsa.

Yan’uwa musulmai! Hadisi ya tabbata daga Abu Ayyub Al’Ansariy R.A cewa: Manzon Allah S.A.W. ya ce “Wanda ya azumci watan Ramadan, sannan ya bi shi da azumi shida cikin shawwal, to kamar ya azumci shekara ce”. (Muslim).

TAKABBALAL LAAHU MINNAA WA MINKUM.

Ibrahim Garba Nayaya, Shugaban Kungiyar Nguru Writers’ Association of Nigeria (NWAN), Jihar Yobe.

07066366586, 08125351694.

ibrahimba182@gmail.com

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai