Babu Adalci A Rika Kiran Mu Shugabannin Tsaro Na Jihohi — Gwamna Yari — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Babu Adalci A Rika Kiran Mu Shugabannin Tsaro Na Jihohi — Gwamna Yari

Published

on


Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya, Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Abdula’aziz Yari Abubakar, ya bayyana cewar bai ga amfanin kiran su da lakabin, ‘Masu kula da tsaro a Jihohinsu’ don haka a cewarsa ya kamata ‘yan majalisun tarayya su cire lakabin ga Gwamnonin.

Yari, ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi ga masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a gidan gwamnatin da ke Gusau, babban birnin Jihar jiya Alhamis.

Gwamna Abdula’aziz Yari Abubakar, ya bayyana takaicin sa kan yadda Majalisar kasa ta ba su Shugabancin tsaron jihohin su, kuma ga shi duk da kudadan da suke kasha wa jami’an tsaron kwalliya ba ta biyan kudin sabulu, kuma Gwamna ba shi da ikon hukunta wani jami’in tsaro a matsayin shi na Shugaban tsaro ko ya yi masa canjin wajen aiki.

‘Don haka babu adalci a rinka kiran mu da Shugabanin tsaro na Jihohi. Don haka muke kira da Shugabancin tsaro a bar wa Shugabannin jami’an tsaro na Jihohi ba gwamnoni ba, idan a kai haka an taimaka mana”, in ji shi.

Jihar Zamfara dai ta dade tana fama da hare-haren ‘yan bindiga wanda ya zama kamar din kwan makauniya duk da kokarin da gwamnatocin da alhakin tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma suka ce suna yi.

 

Advertisement
Click to comment

labarai