Connect with us

LABARAI

’Yan Bindiga Sun Kashe Wani Darakta A Jihar Kwara

Published

on


A halin yanzu jami’an rundunar ‘yan sanda jihar Kwara na karkarde lungunan garin Ilori domin gano gungun ‘yan bindigan da suka kashe wani Darakta a ma’aikatan tsare tsare da tattalin arziki  na jihar Mista Bictor Kayode Dada, ana kyatata zaton wasu gungun ‘yan bindida su biyar ne ciki har da mace suka kashe shi ranar Laraba a cikin garin na Ilori.

Bayani ya nuna cewa, Mista Dada, dan shekara 50, na zaune a ofishinsa ne a unguwar Lajoorin dake cikin garin Ilori inda ka yi masa waya ana bukatar ya zo unguwar Airport road, nan take ya sanar da abokanan aikinsa, ya kuma kama hanyar zuwa inda ake kiran nasa.

Da zuwansa unguwar Airport road din, sai daya daga cikin ‘yan bindiga ya ci gaba da tatauna dashi ya kuma bukaci ya shiga motar sa inda suka fara tafiya har zuwa karshen layin, yayin da kuma wata motar na biye da motar da yake ciki, bayanin ya kuma ci gaba da cewa, daga nan ne sai motar ta tsaya inda ‘yan bindigan suka, fito suka dirarra masa.

Majiyar ya kuma ce, an lura da alamomi a jikin mamaci na kokarin da ya yi na kubutar da kansa daga hannun maharan amma sun fi karfinsa, inda suka mukushe shi.

Sun murkushe shi ne suka kuma zuba masa sinadarin acid baki da wasu sassan jikinsa. Daga nan ne aka jefa gawarsa a cikin maotarsa aka kuma tuka maotar zuwa bakin titi inda suka kulle gawar a cikin motar.

Macen dake cikin ‘yan ta’addan ne ta kira wayar matar mamacin da misalign karfe 4 na asuba, inda take shaida mata cewa, ta je hanyar Airport ta dauki gawar mijin nata.

‘’Daga nan kuma suka goge dukkan lambobin da suka ui amfani dasu a cikin wayar kafin su tafi su bar gawarsa. Basu dauki komai a cikin motar ba, a kwai kuma kudade da abubuwa masu daraja a cikin motar dukkansu na nan daram” inji majiyar tamu.

“A kwai alamomi a jikinsa dake nuna cewa, sun yi bata kasha da maharani, don kuwa daman shi karkarfa ne, amma ‘yan bindigan suma suna da karfi, kuma babu yadda mutum daya zai iya wa mutane da yawa”

‘’Allah ne kadai ya san abin daya wakana tsakaninsa da wadanna mutanen”

Bincike ya nuna cewar, za a yi jana’izarsa ne garin Oro-Ago, ta karamar hukumar Ifelodun ranar 24 ga watan Yuni 2018.

Da yake tsokaci a kan lamarin, jami’in watsa labaran rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, DSP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

‘’Lallai an sanar da ofishina a kan lamarin, abin na da matukar ban mamaki , mun fara bincike mai zurfi a kan lamarin, yana daga cikin abin da muka tatauna a taronmu nay au da safe” inji shi.

 

 

 

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai