Connect with us

LABARAI

Yadda Aka Kammala Zaben Shugabannin APC Lafiya Haka Za A Yi Na Kasa -Nura GT

Published

on


Manufofin shugaban kasa Muhammadu Buhari ga cigaban tattalin arzikin kasar nan shi zai sake baiwa jam’iyyar APC damar sake lashe zabuka masu zuwa domin duk wanda ke kishin kasar nan yasan zuwan gwamnatin Muhammadu Buhari an samu canjin. Dan majalisar dokokin jihar Neja mai wakiltar Kontagora ta biyu, Hon. Nura Garba GT ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai.

GT yace barnar da aka tafka shekaru sha shida ya sanya kasar nan a halin da ta samu kanta wanda sai bayan zuwan Baba Buhari abubuwa suka fara daidaita, a baya tattalin arzikin kasar ya samu kanshi a wani hali wanda tilas tasa aka matse bakin aljihu, duk dan Najeriya shaida ne cewar abubuwa sun fara daidaita a halin yanzu.

Ka duba ko zaben shugabannin jam’iyya kadai an samu nasara wanda sabanin baya da za ka ga ana fasa kawuna, wanda wannan nasarorin ya ta’allaka ne da irin manufofin jam’iyyar APC. Ina da yakinin ‘yan Najeriya sun gamsu da manufofin gwamnatin nan daga sama har kasa, domin in ka kwatanta halin da gwamnatocin jahohin suka samu kansu, ba dan gudunmawar da suka samu daga gwamnatin tarayya ba da wasu ba su iya kai bantensu ba.

Jihata ta isa misali, domin talaka ya shaidi irin kokarin da maigirma gwamna ya ke yi dangane da ayyukan raya kasa, domin bangaren kimiyya duk dan jiha shaida ne akan namijin kokarin da aka yi wajen samar harsashe akan su, makarantar kimiyya ta Maryam Babangida da ta Izom kowa ya shaidi irin gyara da kulawar da suka samu, haka idan ka dawo bangaren kiwon lafiya gwamnatin jiha ta yi kokarin gyara tare da bunkasa wasunsu zuwa abin alfahari musamman yankunan karkara, ka ga ke nan manufar jam’iyyar APC itace kokarin dawo da mutane akan tunaninsu, kan haka gwamnatin jiha karkashin Alhaji Abubakar Sani Bello ta bullo da shiraruwa na dora matasa akan duga-dugansu ta hanyar horar da su ayyukan hannu mabanbanta, ke nan idan mutum yace gwamnati ba tai komai ba, sai mu dauka tamkar yana adawa da cigaban da ake samu ne a jiha ba wai ita gwamnatin ba.

Ina jawo hankalin jama’a kan baiwa gwamnatin tarayya da ta jiha musamman gwamnatocin APC hadin kai dan ganin kasar ta samu nasara akan yaki da rashawa da satar kudin gwamnati, dan da haka ne kawai za a iya dawo da kasar nan akan turbar da ta da ce.


Advertisement
Click to comment

labarai