Connect with us

RAHOTANNI

Madaki Ba Hadimin Magu Ba ne: Zargin Karbar Cin Hanci Na Milyan Hudu Ba Shi Da Tushe -EFCC

Published

on


Kawo yanzu,  hankalin hukumar yaki da cin-hanci da yi wa tattalin arziki zagon kasa wato EFCC a takaice,  ya kai ga wani rahoton da ke ta karakaina mai taken  “Dankasuwa Ya Zargi Hadimin Magu Da Karbar Naira Milyan Hudu”, kamar yadda yake kunshe cikin jaridar Banguard ta ranar 9, ga watan Yunin 2018 wanda kuma aka yada a kafofin yada labarai da dama.

Rahoton ya nuna cewa wani mai suna Abubakar Madaki ma’aikaci a hukumar EFCC da aka ayyana a matsayin hadimin shugaban hukumar,  cewa ya karbi nagoro har naira milyan 4 a hannun Abdulhamid Mahmud Zaria wanda ke ci gaba da fuskantar biciken rashawa don a ba shi beli.

Da wannan hukumar ke bayyana wa duniya karara cewa babu kamshin gaskiya a cikin wannan zargi wanda aka shirya domin bata mutunci da martabar Madaki  wanda kwararre ne a kan aikinsa.

Labarin da ke yawo a kafofin yada labarai shi ne labarin nan na kanzon kurege wanda Zari da jama’arsa suka tsara don shafa wa Madaki kashin kaji tare da zubar masa da  mutunci a idon duniya.

Yana da kyau jama’a su sani cewa,  Zari ya yi ikirarin Madaki ne ya kitsa binciken da ya kai hukumar EFCC ta cafke shi. Bayan samun belin da ya yi, ba tare da bata lokaci ba Zari ya dauki matakin yada Madaki a wasu kafafen yada labarai yana bata shi tare da kakaba masa zargin saye rabin kasar garinsu Keffi a kan kudi naira bilyan goma. Haka nan,  ya zargi Madaki da mallakar wasu manyan gidaje guda biyu a cikin birnin tarayya Abuja wadanda aka kiyasta tsadarsu ta kai kimanin naira milyan 250.

Ganin haka ne ya sa hukumar ta EFCC,  a bisa tsarin dokokinta ta sunkuya bincike a kan wadannan zarge-zargen da aka dora wa madaki inda a karshe ta gano cewa babu gaskiya a cikin lamarin.

Ganin matakin kakaba masa zargi da ya dauka bai yi tasiri a kan Madaki ba,  hakan ya sa Zari ya sake shirya masa wani sabon tuggu ta hanyar rubuta takardar korafi a kansa zuwa ga rundunar ‘yan sanda ta Jihar Nasarawa yana mai zargin cewa Madaki da wani dan’uwansa sun hada kai suna neman hallaka shi yayin watan Ramadana na 2017.

Wannan ya sa aka tsare Madaki na yini guda a ofishin ‘yan sanda kana daga bisani aka mika batun ga babban ofishin ‘yan sada da ke Abuja domin zurfafa bincike. Tuni dai ofishin ‘yan sandan ya kammala bincikensa tare da mika sakamakon binciken zuwa ga ofishin alkalin alkalai na kasa da kuma ofishin ministan shari’a.

Bayan da Zari ya fahimci cewa hedikwatar ‘yan sanda ta tsoma baki ciki lamarin hakan ya sa ya garzaya zuwa Lafia babban birnin Jihar Nasarawa inda ya sa aka cafke wasu ‘yan’uwan Madaki su hudu ciki har da wani dattijo dan shekara 76 mai suna Hashimu Sale,  wanda daga bisani ya rasa ransa a gidan yari yayin da yake tsare. Kazalika,  Zari ya bukaci lauyansa Mike Ozekhome ya maka EFCC da Madaki a kotu don ci gaba da tuhuma. Duk da dai an kai wani matsayi da ya bukaci kotu a kan ta bada umarnin dakatar da ci gaba da binciken da ake yi masa amma kotu ta ki amincewa da haka,  don haka ya daukaka batun zuwa kotun dukaka kara.

Ya zuwa yanzu dai Zari ya sake sabon salo ta hanyar kitsa wa Madaki wasu sabbin zarge-zarge. Inda yake neman duniya ta aminta da cewa an bukace shi da ya bada cin-hanci har naira milyan 4 don a bada belinsa daga hannun hukumar da ba a san ta da halin rashawa ba.

Abin da ma ya kara sha-shantar da zargin shi ne cewa, ba Madaki ne jami’in da ke kula da binciken Zari ba,  hasali ma ba ya daga cikin tawagar da ke kula da binciken baki daya. Don haka wasa da hankali ne kawai a ce wai jami’in da aiki bai shafe shi ba ya kasance shi ke neman a ba shi cin-hanci don bad belin wanda ake zargi.

Idan kuwa Zari ya ci gaba da matsin lambar cewa sai da ya bada cin-hanci kafin ya samu beli,  kenan ya zama wajibi a kansa ya bayyana lokacin da ya mika kudin da wurin da aka karbi kudin hada da yanayin da ya bada kudin, sannan kuma wane ne ya karbi kudin gami da shaidun da suka shaida harkallar duk ya bayyana su.

Da alama cewa Zari ba shi kadai yake wannan aikin ba.  Don kuwa wasu bayanan sirri da EFCC ta samu sun nuna cewa rohotannin bogi da aka yada a kafafen yada labarai wani babban lauyan kasar nan ne ya dauki nauyin haka wanda shi ma a yanzu haka ya fuskanci bincike.

Manufar da ake son cimma a wannan lamari a bayyane take,  wato don cin zarafin Madaki da kuma hukumar EFCC ne kawai sai kuma neman biyan diyyar bata suna idan magana ta kai kotu a kan tuhumar wanda ake zargi.

Yana da kyau a sani cewa EFCC ta nazarci wannan kutungwilar yadda ya kamata, sannan za ta so ta yi amfani da wannan dama wajen kira ga kafafen yada labarai da su kula su daina barin ana amfani da su wajen yada rahotannin bogi. Sannan daga yanzu,  hukumar EFCC ba za ta bata lokaci ba wajen dukar matakin shari’a a kan duk wata kafar yada labarai da ta sa kanta cikin irin wannan hali mara kyau.

 

Domin kore duk wani kokwanto,  Madaki wanda shi ne jagoran sashen kula da tattalin arziki na hukumar EFCC ba hadimin Ibrahim Magu ba ne, kuma bai taba zama hadimin wani ba kafin wannan lokaci. Kokarin bayyana shi a matsayin hadimin Magu wata manufa ce kawai da babban lauyan nan ke da ita da kuma neman cimma shugaban EFCC Ibrahim Magu.

Da wannan, ake kira ga al’umma da su kawar da kansu daga labaran bogi,  tare da sanin cewa babu wani abin da za a aikata da zai yi wa hukumar EFCC tarnaki ya hana ta ci gaba da gudanar da bincike-bincike da taken kan gudanarwa har zuwa karshensu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai