Atletico Madrid Ta Amince Da Siyan Thomas Lemar — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Atletico Madrid Ta Amince Da Siyan Thomas Lemar

Published

on


Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid dake kasar ta Sipaniya ta amince da siyan dan wasan kasar Faransa dan kungiyar kwallon kafa ta Monaco, Thomas Lemar akan kudi fam miliyan 52.

Kungiyoyin Arsenal da Liberpool ne dai a baya suke zawarcin dan wasan mai shekaru 22 a duniya wanda yakoma Monaco daga kungiyar Caen shekaru biyu da suka gabata kuma a shekararsa ta farko ya taimaka Monaco ta lashe kofin kasar Faransa sannan taje wasan kusa dana karshe na cin kofin zakarun turai.

A shekararsa ta farko a kungiyar ta Monaco ya zura kwallaye 14 sannan kuma ya taimaka an zura kwallaye 17 wanda hakan yasa kasar Faransa tafara gayyatarsa domin ya wakilceta a wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya.

Idan har cinikin ya kammala Lemar zai hadu da takwaransa na Faransa, Antonio Griezman wanda ake tunanin zai bar kungiyar zuwa Barcelona amma idan ya yanke shawarar cigaba da zama za su hadu a kungiya daya.

Lemar da Griezman dai a yanzu haka suna kasar Rasha suna shirye shiryen fara gasar cin kofin duniya inda kasar Faransa zata fara buga wasa da kasar Australia a ranar Asabar kafin kuma daga baya ta buga da kasashen Peru da Denmark.

 

Advertisement
Click to comment

labarai