An Yi Wa Manchester United Tayin Dan Wasa Beratti — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

An Yi Wa Manchester United Tayin Dan Wasa Beratti

Published

on


Rahotanni daga kasar Faransa sun bayyana cewa wakilin dan wasa Beratti yayiwa United tayin dan wasan idan suna son siyansa a kasuwar siye da siyar da ‘yan wasan da aka bude a wannan watan bayan da dan wasan ya nuna sha’awarsa na barin kungiyar.

Mai koyar da kungiyar ta Manchester United dai yana kasuwa domin siyan dan wasan tsakiya bayan da kungiyar ta amince da siyan dan wasa Fred dan kasar Brazil yanzu kuma yana neman karin dan wasan tsakiya

A karshen kakar data gabata ne dai dan wasan kungiyar, Macahel Carrick yayi ritaya daga buga kwallo wanda hakan yake nufin kungiyar tana bukatar siyan dan wasan tsakiya domin maye gurbinsa sannan kuma dan wasa Maroune Fellaini yana shirin barin kungiyar.

A kwanakin baya dai an bayyana cewa dan wasa Marco Beratti yana daya daga cikin yan wasan da Mourinho yake zawarci domin kara karfin kungiyar a kakar wasa mai zuwa sannan kuma wakilin dan wasan yace dan wasan a kasuwa yake.

Sabon mai koyar da kungiyar PSG, Thomas Tuchel ne dai ya aka bayyana cewa yace da dan wasan ya rage kiba dalilin dayasa dan wasan yake ganin baza su shirya da sabon kociyan ba kuma tuni yafara neman hanyar barin kungiyar.

Advertisement
Click to comment

labarai