Kano Ta More Gwamna Irin Ganduje — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

HANGEN NESA

Kano Ta More Gwamna Irin Ganduje

Published

on


Mutane suna amfani da zahiri ne, abin da ya bayyana shi ne mutane kan yanke hukunci dashi, lokacin da Tsohon Gwamna Kwankwaso ya bar gadon mulki zuwa sanata, al’ummar Kano sunta tunani da zulumin anya Ganduje zai iya shimfida irin ayyukan da ya aikata wa kanon kuwa?

Ga duk mazaunin jihar kano a yanzu idan ya dubi irin ayyukan da Ganduje ya aikata dole ya yaba masa, ba don komai ba saboda ribar siyasar talaka a yanzu ita ce a shimfida masa ayyuka ya gani a kasa. Hakan kuwa ya tabbata jihar kano domin abin alfahari ne a Kano a ce Ganduje ya dora irin ayyukan da Kwankwaso yabari, har ma ya karashe wasu daga ciki, a nan idan dai ana maganar dimokradiyya ba wai adawar siyasa ba, ya cancanci jinjina matuka.

Kowa ya san irin yadda hanyar kofar ruwa take da cunkuso da cakudi, da yawan mutane kan shafe awowi kafin su kai inda suke son kai wa ta kowace hanya ka biyo, walau ta kurna ko kuma titin da zai kai ka zuwa filin jirgi ko kuma kofar ruwa, samar da gadar kasa a kofar ruwa babbar hikima ce wacce kowane dan kano zai yi alfahari. Haka ta fanshekara wacce tana daga cikin manyan ayyukan da tarihi ba zai manta Gwamna Ganduje ba.

Jihar kano akoda yaushe hazikin Gwamna take bukata, duk da rudun siyasa na jihar, amma babbar siyasar jihar itace taga ayyuka akasa, itace mafi yawan al’umma a kasar, ga manyan kasuwanni na yau da Gobe. Yadda aka gyara kasuwar kantin kwari shi ma wani abin azo aganine da gwamnan yayi, domin tuni manyan biranen duniya da ake dabalbalar kasuwanci suke da tsari da kyawun shiga, yadda akayiwa wasu guraren a kasuwar kwari irin sune muke gani ga manyan biranen da ake hada-hadar kasuwanci, ga rage cinkoso ga kuma samar da ingantacciyar hanyar motoci batare da danne wa masu tebura hakkinsu ba.

Duk da cewar kano garine na noma, amma yadda Ganduje naga yana kula da manoma shi ma wani abu ne da hakan zai kara bunkasa noma a jihar, bada tallafin kusan miliyan dari ga masu noman shinkafa da alkama ya kara karsashi ga manoman, musamman yadda abaya sai dai abada rance ga wasu tsiraru kuma da kananun kudi, amma kebanta wasu domin su daukaka abun shi ne hanya mafi sauki. Ga samar da famfon bada ruwa sama da dubu biyar ga manoman rani, wannan ma wani abin alkairi ne da manoman zasu dade suna amfana sannan an kara musu karsashi wajen ayyukan su, ba kamar abaya ba da aka barsu da jari kadan da kuma siyawa kansu duk abubuwan amfani, wannan shiyake sanya karancin noman da samar da kayan amfanin noman a saukake.

Duk da har yanzu al’umma na kumfar baki harkar ilimi, bawai ina yabonsa ta kowane bangare bane, amma kokarin samar da bencinan zama ga wasu firamare ya kara samar da sauki, da kuma sauran kayan bukatar dalibai musamman a jami’ar Sa’adatu Rimi bayan karashe musu wasu ayyuka. Yaranmu da kannenmu da suke karatu a jihar kano suna jin dadin yadda kullum ake samar musu da kayan bukata da daliban firamare da sakandare ke bukata. Ga kuma karin fannonin karatu da za a yi a Jami’ar Sa’adatu Rimi da kuma makarantar Poly, hakan zai kara bada dama ga al’ummar jihar kano sukara samun gurbin karatu, da kuma rage yawan cinkoso a sauran makarantu na jihar.

Hakika Ganduje yaci sunan sa na Gandun aiki, kuma ko cikin manyan gwamnonin kasar nan zaka sashi sahun gaba wajen masu aiki ga talakawansa, bawai nuna adawa ko kuma banbancin jam’iyya ba, amma ganduje ya cancanci jinjina a jihar ta kano, kuma bai bada kunya ba yadora daga inda kwankwaso ya ajiye har ma ya kara da wasu abubuwan, musamman yadda aka dauki sama da yaran fulani guda dari shida zuwa kasar turkiyya don karatu acan.

Bamu da inda yafi kano bayan kasar mu nijeria, dole muyi marhaban da duk wanda keda kishin kano da kuma kokarin kyautatawa jihar, banbancin siyasa da yawan lokuta kan dakushe irin ci gaban da jihar ta samu. Musamman fadace-fadacen bambancin siyasa, wannan kadai hanya ce da ke kara dakushe ci gaban jihar kano. Akullum abin alfaharin dan kano shi ne waye zai kula da talakawan ciki, waye zai kare mutuncin su ya kuma shimfida musu ayyukan raya birni da karkara, wanda zai karawa fitilar kano haske a idanuwan sauran jihohin kasar nan, wadanda su ka san kano tai musu nisa, kuma ita ke haskaka saura ta wajen ilimi, kasuwanci da yawon bude idanu.

Idan har irin ayyukan da Ganduje zaici gaba da shimfida wa kenan a kano, babu tantama mutanen kano zasu kuma kara masa kuri’unsu don komawa kan mulki akwai zagaye na biyu. Alfaharin mu Kano, farin cikin mu kano, dole ne mu yi maraba da duk wanda zai kara haskaka tauraruwar jihar kano.

Allah Ubangiji ya kara daukaka mana jihar kano.

Allah ya daukaka NIJERIYA Amin.

 

Advertisement
Click to comment

labarai