Gwajin Jini Zai Iya Nuna Ko Za A Haifi Bakwaini -MASANA — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KIWON LAFIYA

Gwajin Jini Zai Iya Nuna Ko Za A Haifi Bakwaini -MASANA

Published

on


Masu bincike a kasashen  Amurka da Danish sun bayyana cewar sun kirkiro da hanyar gaajin jini mai inganci wanda zai iya bayar da tababci zuwa har kashi tamanin akan cewar ko mai juna biyu zata iya haihuwar bakwaini.

Sun bayyana hakan ne a ranar alhamis data gabata, sai dai sunyi nuni da cewar, ya kamata a kara zurfafa binciken kafain a kamma gwajin, inda suka yi nuni da cewar binciken zai ya kawar da matsalolin da za a a iya fuskanta da kuma rage su wajen haifar miliyoyin bakwaini a fadin duniya.

Kamar yadda wata mujallar kimiyya ta ruwaito, gwajin kuma za a iya yin amfani dashi wajen tabbatar da ranar da mai juna biyu zarta haihu wanda kuma zai kasance abin dogara kuma marar tsada.

Dabarun na gwajin yana taimakwa sasssan jikin mai juna biyu kamar na kwayoyin halittar da sauran su.

A cewar wani  babbba akan kiwon lafiya Mads Melbye, kuma farfesan da ya kawo ziyara a jami’ar Stanford har ila yau babban jami’ai  a cibiyar Statens Serum dake Copenhagen, “ mun gano cewar, akwai kwayoyin halitta da yawa a jikin mai juna biyu da zasu iya janyo mata haihuwar bakwaini.

Shi ma wani mai bincike kuma farfesa mai suna Stephen Kuake dake jami’ar wanda ya jagoranci tawagar kirkirar gwajin jini a shekarar 2008 a yanzu kimanin masu juna miliyan uku a duk shekara suna amfana da gwajin.

Haihuwar bakwaini a kasar Amurka ya kai kashi tara bisa dari wanda wannan shine mafi yawa a duniya wajen mutawar yara kafin su kai shekaru biyar da haihuwa.

A cewar wani rahoto, tun dai kafin zuwa yanzu wasu gwaje –gwajen na haihuwar bakwaini, ammasun fi aiki ne akan mai juna biyun da ta shiga cikin matsala so sai wadda kuma ya kai kashi ashirin.

Kafin a kirkiri yin gwajin jini, masu bincike sun dauki jinin mata masu juna biyu su talatin da daya daga kasar Danish  don auna kwayoyin halittar su, inda hakan ya zasu damar gano alamomi na hadarin haihuwar bakwaini.

Bayan an zurfafa binciken a karshe gwajin ya shiga kasuwa , inda masu binciken suka bayyana cewar, za a iya amfani dashi a karkara don amfanin al’ummar ta karkara.

Advertisement
Click to comment

labarai