Connect with us

LABARAI

Hakkin Dan Adam:  Rundunar Soji Ta Bukaci Al’umma Su Kai Rahoton Duk Sojan Da Ya Ci Mutuncinsu

Published

on


Rundunar Soji ta ce ba za ta lamunci duk wani halin rashin da’a daga duk wani jami’inta ba, inda ta bukaci ‘Yan Nijeriya da su kai rahoton duk wani Sojan da ya taka masu hakki, ko ya nemi cin zarafinsu gare ta haka siddan.

Mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar, Birgediya Janar John Agim, ne ya bayyana hakan cikin wata tataunawa da ya yi da mnaema labarai a Abuja. Inda ya shaida masu cewa, rundunar ta Soji tana da hanyoyin ladabtar da duk wani jami’i nata da ya saba dokar aiki.

Ya karyata rahoton kungiyar ‘Amnesty International,’ kan ayyukan Sojojin a nahiyar Arewa maso gabashin kasarnan, ya ce, ai rundunar nasu tana da hanyoyin ladabtar da duk wani jami’i nata da ya sabawa dokar aikin nasu.

“Ba yanda za ka tara Sojoji kamar namu nan ba tare da ka sami wani daga cikinsu yana ketare iyaka ba. Lokacin da nake Maiduguri, na ga wasu matsalolin irin wannan, wadanda kuma Kotunan Soji na musamman suka yi hukunci a kansu. An sami wani Soja da hakka siddan ya sa bindiga ya harbe wasu fararen hula da aka ceto har lahira, nan take aka yi ma shi shari’a, aka kuma yanke ma shi hukuncin kisa. Duk wani Sojan da ku ka ga ya aikata abin da ya sabawa doka, ku kawo mana rahotonsa.

Agim ya ce, a yanzun haka dai babu wata karamar hukuma da ke hannun Boko Haram.

Sai dai ya ce, dajin Sambisa, daji ne mai fadin gaske, domin ya yi fadin Jihar Legas sau goma.

Kakakin rundanar Sojin ya yi nuni da cewa, kasantuwan fadi da rashin tsaron da ke kan iyakokin Nijeriya ne ya sanya ‘yan ta’addan ke samun saukin kurdowa.

Da yake bayanin yadda suke wayarwa da ‘yan ta’addan da suka sallama wuya kai, Agim ya ce, suna yin hakan ne ta hanyar wani shiri nasu na musamman da suke gudanarwa a kansu a Bauci.

Ya kuma yi kiran samar da hadin kai daga manema labarai, Agim ya ce, yayata labaran ne ke kara ruruta ‘yan ta’addan.

“Hanyar kadai da za ka yi maganinsu ita ce, ka takaita yin magana a kan aikace-aikacensu.

A watan jiya ne dai kungiyar, Amnesty International,’ ta zargi dakarun Sojin Nijeriya da ke yaki da ‘yan ta’addan na Boko Haram, da cin zarafin fararen hula.

Amma fadar Shugaban kasa da rundunar ta Soji sun bayyana rahoton na Amnesty da cewa, zargin ba hujja.

Ya kuma yi gargadin cewa, ire-iren wannan rahotannin za su iya sanyaya gwiwar dakarun nata, su kuma cutar da yakin da ake yi da ‘yan ta’addan.

Shi ma babban mai taimakawa Shugaban kasa kan harkokin manema labarai, Garba Shehu, cewa ya yi, rahoton ba shi da wata hujjar tabbatar da shi, don ba wani bincike aka yi ba kafin a bayar da shi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai