Connect with us

LABARAI

Shirin N-Ship Ya Ci Taran Asibitoci Shida A Karamar Hukumar Dass

Published

on


Shirin Babban Bankin Duniya na bayar da tallafin hanun jari domin inganta kiwon lafiya a Nijeriya wato N-Ship ya ci taran cibiyoyin kiwon lafiya shida daga cikin guda goma sha shida da suke cin gajiyar shirin a cikin karamar hukumar Dass, a sakamakon saba wa sharuda da ka’idojin shirin.

Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da shirin ya sake kudi naira miliyan talatin da hudu da dubu dari biyar da casa’in da bakwai da naira tamanin da uku (34,797,83m) domin bayar da tallafi ga cibiyoyin kula da lafiya guda 16 a zangon farko na wannan shekarar.

To; sai dai za a cire naira miliyan shida da dubu dari bakwai da naira tamanin da uku (6,700,83) daga cikin wannan adadin a sakamakon sakaci da aiki da cibiyoyi shidan suka yi da aikin da ke gabansu.

Ko’odinetan shirin N-Ship Dakta Adamu Muhammad shine ya bayyana hakan a yayin wani taron kwamitin tattara aikin a karamar hukumar ta Dass da ke cikin garin Bauchi.

Cibiyoyin kiwon lafiyan da aka dauki matakin hukunci a kansu, sun hada da Bagel, Dull, Dut da ma babban asibitin Dass.

Dakta Adamu Muhammad ya ce an dauki wannan matakin ne daidai da yadda ka’idan shirin ya tsara, kana ya kuma sha alwashin daukan mataki mai tsanani akan dukkanin wani asibitin da aka same shi da yin aringizo a cikin shirin.

Ta bakin Ko’odinetan shirin “Matsalolin da aka samu shine, idan misali ka ce ka biya mata goma sun zo sun haihuwa a asibitinka jami’anmu za su zo su duba fayel-fayel su ga shin akwai wadannan mata goma da ka shaida mana. Idan masu dubawa suka gani, za a eh haka ne za kuma su bayar da rahoton cewar guda goma eh haka ne.

“Bayan wadannan sun gama nasu binciken, akwai kuma wasu jami’an da suma za su zo domin bincika, su kuma za su bi jama’an da aka ce sun haihuwa a asibitin har unguwarsu, za su shiga cikin unguwa su ce a nan unguwar akwai wane-wane mai suna kaza, idan an sameshi sai a tambayeshi irin abun da aka masa, ya yi daidai da rahoton da aka rubutu a asibitin daga nan sai mu amince kan rahoton,” In ji shi.

Kwamishiniyar lafiya ta jihar Bauchi Dakta Zuwaira Ibrahim Hassan wacce ta samu wakilcin jami’in shirin ceto rayukan mutum miliyan daya na jihar Bauchi Alhaji Yakubu Abdullahi Zakshi, ta ce kodayake hukunci ba abu ne na jin dadi ba, amma an yi hakan ne domin ya zama iznina ga sauran.

“Ai shi shirin N-Ship ba wai yana magana ne akan yawan wadanda suka yi jinya ba, akwai bukatar ka nuna gaskiya ma a cikin aikinka, idan ka nuna rashin gaskiya aka dau hukunci a kanka hakan ya yi daidai,” A cewarta.

Darakta kula da lafiya a matakin farko na karamar hukumar Dass Suleman Abdu Kirfi ya nuna gamsuwarsa kan kudaden da aka amince za a raba wa cibiyoyin kiwon lafiya 16 da suke amfana da shirin ta N-Ship a karamar hukumar, yana mai shan alwashin tsaftace shirin.

 


Advertisement
Click to comment

labarai