Nijeriya Ta Biya Jiragen Kasashen Waje Dala Miliyan 600 –IATA — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Nijeriya Ta Biya Jiragen Kasashen Waje Dala Miliyan 600 –IATA

Published

on


Ranar Talata ce kungiyar sufurin sama ta kasa da kasa , ta jiragen sama ,ta  maido da dala milyan 600,wanda mallakar jiragen da suke zurga zurga zuwa na kasa da kasa, wadanda suka hadu da wata matsalar rashin kudaden waje.

Babban jami’i na IATA Mr Aledandre de Juniac akan hanyar sadarwar kungiyar ta yanar gizo, ya bayyana hakan ne a lokacin da ake taro na 74 na kungiyar IATA, wanda na shekara shekara ne a Sydney Australia.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya bada rahoton cewar su kudaen sun kunshi , jiragen saman, sayar  da tikitin tafiya, da kuma sauran wasu al’amura, wadanda ita kasa ba zata iya yi ba, saboda faduwar frashin man fetur din da ake sayarwa kasashen waje, a karshen shekarrar 2016, da kuma farkon shekarar 2017.

Kamar yadda de Juniac ya kara bayyanawa ‘’ Mun samu cin riba bada dadewa ba.’’ Naira milyan 600 a Nijeiya an gama da wannan, bayan haka kuma muna da dala milyan 120, wadannan kudaden an same sune da kudaden da ake dasu a Angola wadanda suka wuce dala milyan 500.

‘’Na ba gwamnatin Angola shawarar cewar su yi aiki dasu jiragen , wannan zai sa su rage yawan bashin da ake bin kasar’’.

De Juniac yayi kira ga gwamnatoci wadanda har yanzu basu samu damar yin hakan ba, su bi dokar  kasa da kasa, da kuma yadda aka kulla ta, wannan zai bas u jiragen damar su amshi kudaden da suke bi.’’

Kamar yadda ya ce, yawan kudaden na jiragen sama da aka tsare a kasashe 16 sun kai dala bilyan 4.9, a karshen shekarar 2017.

Ya kara bayanin cear biyar daga cikin kasashen shida , wadanda jiragen saman suke binsu sun hada da Benezuela ( dala bilyan$3. 78 ) Angola(  dala milyan $386) Sudan  (dala milyan $170)Bangaladesh ( dala milyan$95) da kuma Zimbabwe ( dala milyan$76 ).

“Abubuwan da za a karu dasu ta hanyar sufurin sama, yana da amfani ga ci gaban tattalin arziki, sufurin sama yana samar da ayyukan yi, da kuma kasuwanci, abinda yana taimakawa mutane su samu rayuwa mai kyau.’’

“Amma kuma jiragen sama suna  bukatar a kara masu kwarin guiwa, wadda zata nuna zasu iya samun damar maido da kudaden da suke bi domin bunkasa kasuwanci a kasashen su.’’

 

Advertisement
Click to comment

labarai