Connect with us

LABARAI

Ni Na Hana Femi Adesina Ya Ragargaji Obasanjo –Buhari

Published

on


Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, ya hana babban mashawarcinsa kan harkokin manema labarai da fadakarwa, Femi Adesina, daga mayar wa da tsohon Shugaban kasarnan, Olusegun Obasanjo, amsa ne kan wasikar da ya aiko masa ta sukar gwamnatin na shi ne saboda, ‘Shekarun Adesina din.’

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne sa’ilin da wakilan kungiyar kamfen ta, ‘Buhari Support Organisation’ suka kai ma shi ziyara a fadar ta Aso, da ke Abuja, a daren Juma’a.

Buhari ya kara da cewa, dalili kuma na biyu da nake ganin babu bukatar a amsa ma wasikar na shi shi ne, Ni da tsohon Shugaban duk daga rundunar Soji ne muka fito.

Sai dai ya ce, Ministan al’adu da yada labarai, Lai Mohammed, wanda ya ki yi mani biyayya kan hakan, ya mayar wa da wasikar martani kyakkyawa.

Ya yi nuni da cewa, amsar da Ministan ya bayar, ta nuna wa ‘yan Nijeriya gaskiyan halin da wannan gwamnatin ta sami kasarnan a lokacin da ta hau karagar mulki a 2015, da kuma irin hobbasan da muke yi na farfado da tattalin arzikinmu da aka yi kaca-kaca da shi.

“Gaskiya na ji dadin zabar wannnan lokacin na watan Ramadan da ku ka yi na ku zo ku gaishe ni kan dan abin da muka tabuka.

“Tabbatacce ne, ina kuma kalubalantar kowa da ya bincika tun daga kasashen Turai zuwa Amurka da kasashen Asiya, a tsakankanin shekarun 2006 da kuma 2014, shekaru 16 na gwamnatin baya, kusan a kullum ana fitar da gangunan danyan mai milyan 2.1 ne, akan farashin dala 100 kan kowace gangar mai,” in ji shi.

Shugaba Buhari ya ce, da gangan ne na ki da na sauya gwamnan babban bankin Nijeriya ko da na karbi mulki, saboda ina so ne na ba shi daman ceto mummunan halin da tattalin arzikinmu yake ciki ne.

Shugaba Buhari, ya nanata yin godiya ga malamansa na makarantar firamare, wadanda ya ce, sune suka kimsa masa da ma sa’o’in sa dabi’u na kwarai, ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari mai yawa a fannin ilimi domin gyara halayen al’umma.

Ya kuma ce, gwamnatin na shi ta yanke shawarar zuba kudade masu yawa wajen samar da manyan ayyukan ci gaban kasa domin magance karancin hakan da ake fama da shi a halin yanzun da nufin hanzarta farfado da tattalin arzikin kasa.

“Yanzun ne muke kokarin samar da ayyukan, Hanyoyi, farfado da sufurin Jiragen kasa, da samar da gamsasshiyar hasken lantarki.

“Da zaran mun kwarara kudi kan samar da manyan ayyuka, kenan za a sami ayyukan yi, a lokacin ne ‘yan Nijeriya kowa zai shiga taitayinsa, ba ma wanda zai damu da ko mene ne gwamnati ke yi, matukar dai kowa na da aikin da yake yi,” in ji shi.

A cewar shugaban, a yanzun haka gwamnatin na shi ta kashe sama da Naira tiriliyon 1.3 kan manyan ayyuka a dukkanin sassan kasarnan.

Ya kuma yi godiya ga wakilan kungiyar kamfen din na shi kan irin sadaukarwar da suke yi, inda ya yi masu nuni da cewa, babu daya daga cikinsu da ya taba fuskantarsa da wata bukata na shi.

A na shi jawabin, jagoran kungiyar, Abba Ali, wanda ya yi ta lissafo ayyukan ci gaban da gwamnatin ta Shugaba Buhari ta aiwatar cikin shekaru ukun da suka gabata, cewa ya yi sun zo ne da nufin jaddada ma shi goyon bayansu a gare shi, su kuma tabbatar ma shi da cewa suna nan a tare da shi.

Ya kuma ce, kawo yanzun kungiyar nasu ta kammala kafa rassanta a dukkanin Jihohin kasarnan 36 da ma kananan hukumomi 774 da ke fadin kasarnan, suna kuma yin duk mai yiwuwa na ganin ya cimma burinsa na sake dawowa mulkin a shekarar 2019.

Paulina Tallen, wacce tana cikin kwamitin amintattu na kungiyar, ta tabbatar wa da Shugaba Buhari goyon bayan daukacin matan kasarnan ne a yayin ziyarar, na ganin tun daga kanshi har daukacin ‘yan takarar Jam’iyyar APC sun kai ga gaci a zabukan 2019.

Sai dai ta yi kira ga Shugaban kasan da ya kara saka matan da suka cancanta a cikin gwamnatin na shi, domin magance matsalar da ake kuka da ita na danne jinsin matan da jinsin maza suka yi a mulkin kasarnan.

 


Advertisement
Click to comment

labarai