Connect with us

LABARAI

Muna Kalubalantar Zaluntar Daukacin ’Yan Nijeriya Ne Ba Kawai Kiristoci Ba, Inji CAN

Published

on


Kungiyar kiritocin Nijeriya ta “Christian Association of Nigeria (CAN)” ta bayyana cewa, fadan data keyi da zalunci da danniya baya tsaya a kan Kiristoci kawai bane amma kokari ne da suke yi domin kare dukkan ‘yan Nijeriya.

Shugaban kungiyar, Mista Samson Ayokunle ne ya yi wannan bayanin a wani taron don karrama marigayi Musa Asake sakataren kungiyar ta kasa, wanda ya mutu rana 11 ga watan Mayu, ya ce, kungiyar zata ci gaba da yaki da dukkan nau’in danniyar da ake yi wa dukka ‘yan Nijeria.

“Muna kalubalantar dukkan danniya ba wai akan kiristoci kawai ba amma a kan dukkan ‘ya Nijeriya”

Lallai mutum zai iya cewa, dole mu fara kare ‘yanuwan mu Kiristoci, amma abubuwa da dama sun rincabe a kasar nan, irin tashin hankalin da ake yi a fadin kasar nan yana da matukar tayar da hankali, zamu ci gaba da Magana a kai, zamu kuma kalubalanci dukkan nau’in nuna banbancin addini da kuma dukkan nau’in danniya da ake yi wa ‘yan Nijeriya” inji Mista Ayokunle.

A nasa jawabin, wani Fasto daga garinsu Mista Mr Asake a jihar Kaduna, mai suna Mista Mathew Owojaiye, ya dora halin da ake ciki a kasar nan ne a kan lallacewar shugabanci daga bangaren Kiristocin kasar nan.

“Nijeriya na fuskantar matsaloli mai dimbin yawa, coci-coci daya kamata ta jagoranci harkar zama lafiya amma a halin yanzu ana rayuwa ne a yanayi mai tsananin tashin hankali, muna kuma fuskantar gwamnatin da bata rungumi ‘yan kasa baki daya a matsayin nata ba. A na tarwatsa garuruwar Kiristoci a yankin tsakiyar kaar nan, ana tarwatsa wad a kona kauyuka, a kullum ana kashe yara da mata ba tare da wani laifi ba.

“Ko dai gwamnati ta ki tsayar da kashe-kashen da ake ti ko kuma masu kisan ‘yan koren gwamnati ne”

“Yadda lamarin yake shi ne, ko dai ‘yan siyasan mu Kiristoci wadanda ya kamata su kare mu sun sayar da ‘yancin namu ne ko kuma suna tsoron yin magana ne”

Mista Owojaiye ya kuma zargi shugaban Kiristoci da kirkiran wannan halin da ake ciki ta hanyar yin gurbatattacen wa’azi a ‘yan shekarun nan.

“Ana saba dokokin Allah ba tare da wani tsoro ba a kullum, munbarin wa’azi yana dauke da manyan zunubi fiye da ko’ina, mun mayar da coci-coci wajen neman kudi, muna wa’azi ne kawai don dadada wa jama’a rai ba don Allah ba”

Ya kuma bukaci shugabannin kiristoci dasu gaggauta fuskantar abin daya hau kansu saboda su samu kancewa daga fadawa fushin Allah.

Shugaannin kiristoci da dama da suka halarci taron sun yaba da jawaban da Mista Asake ya yi a kan ci gaba da kuma halin da Kiristocin Nijeriya ke ciki, sun kuma hori sauran jagororin kiristocin su yi koyi da shi wajen koma wa yin hidima ga Allah shi kadai.

 


Advertisement
Click to comment

labarai