Connect with us

LABARAI

Marayu Sun Samu Tallafin Kaya Sallah A Legas

Published

on


Kungiyar bayar da tallafi ga marayun ta kasa a karkashin kungiyar izalatul bidia walkamatus sunna ta jihar legos ta bayar da tallafin kayan sawa ga yara marayu sama da dubu daya da dari biyar a jihar Legas shugaban kungiyar Alhaji Umar Lawan Atana ya bayyana wa manema labarai hakan a offishin kungiyar dake unguwan Jokshon Alfa Lilla Agege Legas, shugaban kungiyar ya ci gaba da cewar sunay wa marayun wanna tallafi ne na kayan abinci da kayan sawa a duk shekara a daidai wanna lokacin da musulmai ke gudanar da bukukuwan sallah karama ko kuma babba domin suma yaran marayun su faran tamasu rai satashi da farin ciki do annashuwa a safiyar sallah kamar kowane yaro.

Alhaji Umar Lawan Atana ya kara da cewar, a kan haka nema ya ce, bari ya yi amfani da wanna dama ya mika sakonsa ga alummar musulmi musaman masu hannu da shuni na jihar Legas dasu rinka kafa kamfanonin da zasu rika sama musu riba ko guzurin zaman lahira kamar yanda suka kafa kanfanonin samun kudi a duniya inji shi, ita wanna kungiyar tana tallafa wa yara marayu ne ta bangare da yawa kamar bangaren neman ilmin boko kona isilamiyya kungiyar na daukar nuayin wasu marayun zuwa wasu makarantu domin su samu tsayawa da kafafunsu.

Da sauran ayyukan alheri da kungiyar ke gudanar wa na tallafawa marayu a cewarsa kungiyar kowane lokaci tana gudanar da irin wadannan ayyukan sai dai kuma tafi kara fadada ayyukan daidai wannan lokaci na azumin watan Ramadan.

Ya ci gaba da yaba wa abokan aikinsa na cikin wannan kungiyar wanda da kokarinsu ne kungiyar ke samun nasarori da yawa bisa ga jajircewar dasu keyi akowanne lokaci ba dare ba rana domin tafiyar da ayyukan kungiyar.

Ya kuma gabatar da godiya ta musamman ga mataimakinsa Alhaji Garban Jabbo Dandakan Hadeja kuma Marafan Agege bisa ga namijin kokarin daya keyi wajan bunkasa harkokin ci gaban wanna kungiyar..

Haka shima Sakataren kungiyar Malam Sha’aibu Adamu Agege da P.A na kungiya Alhaji Hassan Agege suma suna taka rawa ta musamman wajen ganin wannan kungiya ta samu ci gaba da ayyukanta na alheri da fatan Allah ya ci gaba dayi mana jagora.


Advertisement
Click to comment

labarai