Connect with us

LABARAI

Kokarin Hon. Goro: Al’umma Na Goyon Bayan Samar Da Kwalejin Kimiyya Da Fasa A Fagge

Published

on


Jama’ar jihar Kano musamman ma al’ummar  karamar hukumar Fagge na nuna matukar goyon bayansu ga kokarin Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Fagge, Kwamred Aminu Suleiman Goro na ganin an gina babbar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta tarayya”Federal Polytechnic” a yankin karamar hukumar ta Fagge.

Wannan kuwa ya biyo bayan kuduri da dan majalisar ya gabatar a majalisar tarayya kan samar da babbar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta tarayya a Fagge, wanda kuma a yanzu haka kudurin ya tsallake karatu na daya da na biyu, har an saurari ra’ayoyin jama’a a kai.

Daya daga cikin masu ruwa da tsaki a karamar hukumar ta Fagge wanda yana cikin tawagar da suka halarci jin ra’ayin a Abuja.Mataimakin Shugaban karamar hukumar, Barista Ahmad Salisu ya ce al’ummar Fagge suna mutukar goyon bayan dan majalisar akan wannan manufa tasa ta raya ilimi da ya gabatar wanda zai amfani al’ummar Kano da ma Arewa gaba daya.

Mataimakin Shugaban na Fagge, Barista Ahmad Salisu ya ce, masu ruwa da tsaki a fagge karkashin jagorancin Shugaban karamar hukumar, Alhaji Ibrahim Muhammad Abdullahi, da shugabannin jam’iyyu na yankin da Shehunan malaman jami’a da sauran bangarorin al’umma ne suka halarci jin ra’ayin wanda aka gabatar a ranar 28 ga Mayun, 2018 a majalisar tarayyya.

Ya ce, tawagar al’ummar Fagge da suka halarci zaman sauraren ra’ayin jama’ar a Abuja kan samar da makarantar sun nuna goyon bayansu sosai ga kudurin dan majalisar tare da nuna cewa hakan wata dama ce ta dada fadada harkar ci gaban ilimi da aikin yi a Fagge.

Barista Ahmad Salisu ya ce, Dan majalisar na tarayya mai wakiltar Fagge, Kwamred Aminu Goro wanda shi ne kuma shugaban kwamitin Ilimin makarantun gaba da sakandare a majalisar, ya yi kyakkyawan tunani kuma hakan zai bunkasa ilimi a Fagge wanda a yanzu haka yankin yana da manyan malaman jami’a da yawa da malaman addini da yara masu tasowa akan harkar ilimi da sana’a.

Barista Ahmad Salisu ya ce, wannan ci gaba ne da yake bukatar goyon bayan kowa a Fagge da jihar Kano da Arewacin kasar nan gaba daya duk za a hadu a kai ba tare da nuna bambancin siyasa ba.

 


Advertisement
Click to comment

labarai