Kamfanin Kasar Chana Zai Zuba Jarin Dala Miliyan 300 A Fannin Samar Da Gidaje A Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Kamfanin Kasar Chana Zai Zuba Jarin Dala Miliyan 300 A Fannin Samar Da Gidaje A Nijeriya

Published

on


Kamfanin da ake kira One Belt One Road, na kasar Chana ya sanar da cewar ta hanyar kamfanin, gwamnatin kasar ta Chana, zata zuba jari na dala miliyan 300  a shirin gina gidaje

masu yawa na Nijeriya nan bada jimawa ba.

Daraktan kamfanin, Mista Steben Kim ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da kamfanin da ake kira Zbecan Homes Estates ya shirya a ranar talatar data gabata a garin Abuja.

Mista Kim yace, kamfanin nasa na One Belt One Road tare da hadin gwaiwar kamfanin Zbecan Homes and Estate wanda a kwanan baya suka rattaba hannun yarjejeniya ta fahimta

zasu gina gidaje guda 5000 a Abuja da kiwayen ta.

A cewar sa, zuba jarin zai kamfanin nasa damar cimma burin manufar kafa kamfanin da aka yi a kasar Chana, inda ya kara da cewar, manufar itace, don a taimaka wajen gudanar da ayyukan da mutane zasu amfana.

Ya ci gaba da cewa, “mun fito ne daga kamfanin da ake kira One Belt and One Road dake kasar  Chana kuma kamfanin da ya zuba jari akan ayyukan da kai tsaye, suka shafi rayukan alummar dake cikin nahiyar  Afrika kuma munzo nan ne don baiwa kamfanin da ake kira   Zbecan akan ayyukan su, musamman na shirin hukumar gina gidaje na ma’aikatan gwamnatin tarayya  (FISH).”

Mista Kim ya kara da cewa, “munyi amanna cewar, wannan aikin zai amfani rayuwar alummar garin Abuja da kuma Nijeriya baki daya kuma zamu iya zuba kudi akan aikin ta hanyar ofishin mu.”

Ya sanar da cewar, zuba jarin ba kawai zai kasance a na kudi bane har da sanya kayan wutar lantarki da na’ura mai aiki da hasken rana da sauran su.

Shima a nashi jawabin, Manajin Darkta na kamfaninin Global Hint Construction na kasar Chana daya daga cikin kamfanonin da za a yi amfani dasu, Mista Aigbe Osagie yace, irin wannan ayyukan tuni, ana kan ci gaba da aiwatar dasu a kasashen Kenya da kuma Angola.

A cewar sa, tuni sun gina sama da gidaje  5000 a kasashen Angola da Kenya, kuma suna son gina makamantan hakan a Nijeriya.

Mista Osagie ya yi nuni da cewar, kalubalen da ake fuskanta wajen yin gini a nahiyar Afrika itace ta yanayin kasar yin gini, inda ya kara da cewa, amma kasar yin gini irin ta Chana tafi kyau a bisa ta kasashen dake  Afrika.

Nicholas Ogbede, Manajin Darakta na kamfanin  Zbecan Homes Estate ya sanar da cewar, jarin da gwamnatin Chana zata zuba, zai taimaka wajen kawar da kalubalen da ma’aikata suke fuskanta na gidajen kwana.

A cewar sa, a bisa kimiyyar da Chana take dashi da ban-da-ban wajen aikin gini zata taimaka wajen samar da ragi na tsadar gini wajen gina gidaje ga ma’aikatan gwamnati ‘yan  Nijeriya.

Ya sanar da cewar, kamfanin Zbecan Homes Estate ya kuma rattaba hannu ta yarjejeniyar fahimta da ofishin shugabar ma’aita ta tarayya don gina gidaje 700 a karkashin shirin gwamnatin tarayya mai suna FISH.

A cewar sa,“muna son mu samar da gidaje masu saukin kudi a wurare masu kyau ga ma’aikata ganin cewar, mafi yawanci suna yo tattaki daga wurare maso nisan gaske zuwa gun aiki a kullun.

Ya sanar da cewar, “a yanzu hakan muna da sama da  5000 da suka nuna suna bukatar gidajen mu kuma mun yanke shawarar yin amfani da shirin gidauniyar gina gidaje na kasa  (NHF) don samar da gidaje ga ma’aikata.

A cewar sa, “muna kuma kan yin kokari wajen tuntbar ma’aikatu da sassa da kuma hukumomi  da zasu samar da kaya don yin gine-gien mu akan farashi mai sauki don mu cimma burin da muka sanya a gaba.

Idan za a iya tunawa,  ‘yan kasar na Chana masu gina gidajen, a cikin watan Afirilun shekarar 2018 ce, suka kawo ziyara Nijeriya don gudanar da bincike da kuma auna kasa dangane da guraren da zasu yi gina gidajen.

 

Advertisement
Click to comment

labarai