Connect with us

LABARAI

Hatsarin Mota Ta Ci Rayukan Mutane Biyar A Nija, Inji FRSC

Published

on


Hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) reshen jihar Nija ta bayyana cewar akalla mutane biyar ne suka mutu a sakamakon wani hatsarin mota da ta auku a ranar Asabar a kan titin Lambata Kwakuri da ke karamar hukumar Gurara.

Shugaban Shiyya na hukumar FRSC, Mr Yusuf Garba, shine ya shaida hakan wa kamfanin dillacin labarai ta Nijeriya a garin Minna a jiya Lahadi, ya ce hatsarin ta auku ne a tsakanin wata mota da kuma tifa.

Ya ce, hatsarin wanda ya hada da wata mota mai launin fari BMW dauke da lamba BWR 264 SR da kuma wata Tifa Scana mai lamba ISR 16 DU.

Shugaban jinyar ya bayyana cewar dukkanin mutane biyar da suke cikin mota BWM dukkaninsu sun mutu, inda ya kara da cewa dayan diraban da ya hatsarin ta rutsa da su wanda ya gamu da munanan raunuka tunin aka kaisa babban asibitin garin Suleja domin kula da lafiyarsa.

Kamar yadda yake bayani, ya shaida cewar hatsarin ta auku ne a sakamakon tsula gudun tsiya da direbobin ke yi a wanda hakan babbar hatsari ne a direbobi.

Yusuf Garba ya shaida cewar hukumarsu ta FRSC za ta ci gaba da bibiyar masu amfani da hanya domin tabbatar da cewar suna bin dokoki da ka’idojin tuki domin kauce wa fadawa cikin hatsari.

Garba ya kuma kirayi masu amfani da titian da suke kokarin bin ka’idojin kan hanya da kuma bin ka’idodin da aka shimfida musu domin kauce wa fadawa cikin hatsari.

“Za mu ci gaba da gudanar da aikinmu na sintiri a dukkanin manyan hanyoyi na tsawon 24 domin tabbatar da kare rayuka da lafiyar direbobi da facinjoji, ta hanyar tabbatar da cewar direbobi suna bin ka’idojin tuki a kowani lokaci,” In ji shi.

Daga nan kuma sai ya nemi mazauna jahar da suke hantsarin kai rahoton aukuwar kowace irin hatsari domin hukumarsu take zuwa domin kai agajin gaggawa don dauke marasa lafiya da kuma wadanda hatsari ta rutsa da su a kowani lokaci.


Advertisement
Click to comment

labarai