Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Neja Za Ta Dau Mataki Akan Gidajen Masha’a A Lokacin Bukukuwan Sallah

Published

on


An bayyana cewar gwamnatin Neja za ta sanya idanu dan hana masu anfani da bukin sallah dan aikata ayyukan masha’a, wanda barin hakan na cigaba da faruwa tamkar take hakkin addini ne. Babban darakta a ma’aikatar kula da harkokin addinai ta jiha, Dakta Umar Faruk Abdullahi ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan kammala sallar juma’a a masallacin juma’ar Bosso Estate da ke minna.

Dakta Umar Faruk ya ce sau tari idan lokacin bukukuwan sallah ya taho wasu kan kange gidaje dan hada mata da maza waje daya ana bata tarbiyar matasa da sunan bukin sallah wanda wannan babbar illa ce a cikin al’umma. Ya kamata mutumin da ya azumci ramadan har tsawon kwanaki ashirin da tara zuwa talatin ya zama na yana kyautata zaton samun gafara da rabo a wajen Allah, domin ramadan ana kyautata karbuwarsa itace dora mutum a hanyar alheri kamar yadda Manzon Allah ya nusar,  maimakon a raya sunnar Manzon Allah wajen ziyarce- ziyarce da sadar da alherai sai kuma ya zama lokaci ne na gurbata tarbiyar matasa da kirkiro hanyoyin tashin hankali a cikin al’umma, masu wajajen masha’a, zamu zauna da su dan nuna masu illar hakan,gwamnati ba za ta lamunci yaduwar miyagun dabi’u ba,  masu wasa da mashin zamu mika aikin hannun jami’an tsaro domin ba komai suke haddasawa ba face barazana da tashin hankali a cikin al’umma.

Dakta ya jawo hankalin jama’a wajen fitar da zakkar kono akan lokaci, ya ce jama’a na cikin wani hali kuma suna neman tallafin ‘yan uwa ya kamata masu hannu da shuni da su fitar da na su zakkar kan kari ta yadda wadanda zasu anfane shi suma suyi tanadi cikin lokaci. Daktan ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari akan irin kokarin da yake yi na farfado da tattalin arzikin kasar ta hanyar yaki da rashawa ya ce lallai manufar shugaban kasa ga kasar nan abin a yaba ne musamman baiwa jami’an soja karfi na karya lagon Boko Haram da baiwa jami’an ‘yan sanda damar yin aikinsu yadda ya kamata ga masu garkuwa da mutane da masu satar shanu.

Dan haka bai kamata jama’a su zura idanu suna kallon gwamnati haka siddan ba, akwai bukatar mu tashi tsaye mune takobi ga gwamnati mu tashi haikan wajen taya gwamnati addu’o’in samun nasara musamman ganin aikin babba ne, a jihar Neja ya zama lallai mu yaba wa maigirma gwamna akan namijin kokarin da yake yi wajen daidaita lamurra a jihar nan, mun san inda aka fito kuma mun san inda ake a yau.

Ina kara jaddadawa Iyaye ya zama wajibi mu tashi haikan wajen inganta tarbiyar ‘yayan mu, akwai bukatar sanya idanu sosai ta lura da abokan mu’amalarsu da yanayin tafiyar harkokin rayuwarsu dan gujewa fadawa hannun bata gari.

 


Advertisement
Click to comment

labarai