Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Neja Ta Samu Biliyan 482 A Shekaru Biyun Farko Amma Ba Aikin Nunawa -ADP

Published

on


Jam’iyyar ADP tayi addu’o’in cika shekara daya da samun rajista a matsayin jam’iyya a jihar Neja. Taron addu’o’in da ya samu halartar ‘yayan jam’iyyar da dukkanin ‘yan takarkaru a zabuka masu zuwa, an yi shi ne a harabar sakatariyar jam’iyyar ta jiha da ke minna.

Tunda farko da yake bayani ga dubban magoya bayan jam’iyyar, shugaban jam’iyyar ta jiha, Alhaji Tanimu Sarki Kwamba ( Dallatun Kwamba) ya ce maganar gaskiya APC ta kasa cika alkawurran da ta yi wa al’umma a a lokacin zabukan da suka gabata saboda tun asali ba jam’iyya ba ce hadakar kungiyoyi ne shi ya sa ba ta da wani ajandar bunkasa tattalin arzikin kasa balle inganta rayuwar al’umma.

Kwamba ya ci gaba da cewar abin da zai baka mamaki, ba wata jam’iyya da ta samu gwamnati a jihar Neja da ta samu kudade kamar irin wanda gwamnatin nan ta Alhaji Abubakar Sani Bello ta samu, domin ko a shekarun shi biyu na farkon mulki kawai ya samu zunzurutun kudi naira biliyan 482 amma ba wani aikin kirki da za ka iya nunawa da aka kashe kudaden nan, to ban ga wani abin da APC za ta nuna a jihar nan da za tai alfahari da shi ba wanda za tace za a iya alfahari da shi nan da shekaru goma masu zuwa.

Ya ce ko shafe-shafen da ake yi na fenti duk yabe domin ayyuka ne wanda gwamnatin da ta shude tayi kuma kowa ya san ta kammala su, su ne kuma yanzu ake bi da sabon fenti sai shataletale cikin garin minna da aka rusa su da makuddan kudade, ya ce yanzu haka wani aikin baban-giwa da gwamnatin ke cewa yana kan yinsa shi ne rushe katangar gidan gwamnati mai tarihi da asali wanda jama’a ba su alfanun rusa shi da sabon katangar da a ke yi a kan shi ba yanzu.

Tanimu ya jawo hankalin gwamnati akan irin bakar siyasar da ta ke kokarin assasawa a jihar wanda yanzu haka gwamnatin ta dakatar da Kwamared Baba Mohammed Wanigi wani malamin makarantar faramare a karamar hukumar Agaie kawai saboda ya bayyana APC gaskiya akan irin kura-kuran da ta ke tafkawa, kuma ta nemi gwamnan da yayi adalci akan Prince Shehu ma’aikacin da aka dakatarwa albashi na a kallan watanni uku akan ya fadi ra’ayinsa dangane ranar murnar dimukuradiyya a Nijeriya.

Sarki Kwamba ya ce akwai bukatar maigirma gwamna da ya sauka akan kujerarsa dan ya kasa cika alkawurran da yayi lokacin yakin neman zaben da ya gabata. Ya ce da alkawari ko rashin alkawari da gwamnan ya ce ya yiwa al’umma jihar akwai bukatar ya fito ya bayyana inda ya kai kudaden jihar wanda zuwa yanzu ba wani abin da zai nunawa al’umma da sunan ci gaba a jihar duk da irin makuddan kudaden da yake samu daga aljihun gwamnatin tarayya, domin jama’ar jiha na bukatar hanyoyi, asibitoci da kayan aiki, nagartattun makarantu da kayan aiki wanda dole sai an inganta wadannan za a samu ci gaba.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, mataimakin sakataren jam’iyyar ta kasa, Alhaji Haruna Usman Dangajere, ya ce lallai maganar tsaro a kasar nan sai dai a mayar da al’amari ga Allah duba da irin abubuwan da ke faruwa a Jihar Zamfara da Kaduna a yanzu, ya ce yanzu a kallan Birnin Gwari da ke iyaka da jihar Zamfara abin ko dai da gangan gwamnatin tarayya ke yi, domin in ka ga irin makuddan kudade da ake sakewa da sunan tsaro a kasar nan dole ne ka jefa ayar tambaya akai.

An ce ana yaki da rashawa, mu kuma a yadda muka fahimci lamarin ana yaki ne da wadanda ake zargin suna karban rashawa amma rashawar na nan tana gudana, domin ya kamata ne a faro daga gida a tabbatar an kakkabe rashawa a cikin al’umma. Maganar gaskiya shugaba Muhammadu Buhari ya kasa kuma jam’iyyar nan a jihar nan tana da ‘yan takara guda biyu yanzu haka daga jihar Neja na shugaban kasa wanda kuma a fadin tarayya Nijeriya za a same su da dama. ADP jam’iyyar siyasa ce da ta zo da manufofin inganta kasa da ciyar da al’ummarta gaba.

Taron dai ya samu kusoshin jam’iyyar na kasa da jiha wanda kuma an kammala shi ranar alhamis din da ya gabata.

 


Advertisement
Click to comment

labarai