Gwamna el-Rufai Ya Gama Da Mu —Shettiman Barnawa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Gwamna el-Rufai Ya Gama Da Mu —Shettiman Barnawa

Published

on


ALHAJI  ABDULAZEEZ MUSA yana daya daga cikin matasa masu fashin baki a harkar siyara Kaduna har da kasa baki daya. Har ila yau, Abdulazeez shine Shatiman Barnawa. A hirar sa da wakilin mu ABUBAKAR ABBA ya yi bayani akan dokar da shugaban kasa Buhari ya sanyawa hannu wadda ta baiwa matasa damar tsayawa takara da kuma yadda gwamana Nasir Ahmed El-rufai ya yi  amfina da na’urar zabe a zaben kananan hukumomi da aka kammala kwanan baya a Kaduna. Ga yadda hirar ta kasance:

Mene ne ra’ayin ka a bisa sanya hannu da shugaban kasa ya yi akan dokar baiwa matasa damar tsayawa takara a kasar nan musamman ganin cewar a dade ana fafutukar hakan?

Ai idanka dubi yadda wannan abin faru, kusan dukkan wani dan  Nijeriya wannan abin ya bashi mamaki, domin an dade ana sa ran hakan amma bai yuwa ba amma sai gashi a cikin ruwan sanyi, mai girma shugaban kasa ya zo ya sanya kudirin ya zama doka. Amma ga cikin abin tsoro ga wannan abin shine, yanzu ana riga an baiwa matasa wannan damar.

Amma ban sani ba ko matsan za su yi amfani da wannan damar ko kuma za su bari a ci gaba da amfani dasu ne yadda aka saba. Kasan tsoron da ake a yanzu shi matashin da aka baiwa wannan damar  baida kudin fitowa takara domin maganar siyasa maganar kudi ce. Amma wasu za su iya amfani da damar su fito dasu don cimma wasu burin su na siyasa. Allah dai ya tsare. Koda yake dan Nijeriya yanzu kansa ya riga ya waye domin idan kace ka tsayar dani don in yi yadda kake so,  toh infa aka zo zabe nan ne za a yi tsiya domin dan Nijeriya yanzu ya yi wayo domin abinda yake so ne ba wanda kai kake so ba kaji gaskiyar magana.

To wanne kira zaka yi ga matasan akan kada su bari wani ya dauki nauyin su tsaya takara don cimma wani burin su na siyasa?

Toh ai kamar yadda na ce ne da farko, su fito suyi abinda ya kamata suyi don wannnan shine lokaci na karshe ga matasan, idan suka karba suka kuma watsar ya rage nasu, idan suka kuma yi amfani da damar sune za su amfana harda wadanda  za su zo a bayan su, amma duk wanda ya fito ya ce zai baka kudi don ya tsayar da kai takara don kai matashin baka da kudin na tsaywa takarar.

Kana ganin idan matasa suka yi amfani da wannan damar za su iya taimaka wa Nijeriya?

Kwarai kuwa, amma ya danganta ne da irin talbiyyra da ka samu ne tun farko domin suna iya abinda ya kamata saboda talbiiyar da suka samu tun daga gidajen su, suna kuma iya yin watsi da hakan domin abin daya daga cikin biyu ne.

Ya kake ganin kamun ludayin matashin da misali aka zabe shi ya zama gwamna ko dan majalisa?

Ai kamar yadda na ce ne in akwai talbiyya yanzu misali in ya kai labara zai yi kokarin ya gyra gaba kaga in suka yi wannan sunyi wa kansu kiyamul lai sai kuma aci gaba da yi dasu in kuwa suka barar toh shi kenan ta kare.

Daga ina kake ganin matasan za su fara ganin cewar basu da kwarewa sosai a siyasar?

Daya daga ciki shine ko kayi karatu domin akaiwa fanni na iya iya siya da kuma na mulki domin a kalla kullum kana zaune kuma kaga anayi data ita siyasa ko ka koya ko kuma kaga anayi sai ka zabi wanda kaga ya yi maka. Sannan kuma matashi zai iya fara daga kasa kamar mukamin kansila, matsalar da ake fuskanta shine, matasan mu suna da gaggawa. Koda yake ‘yan adawa suna fakewa da rahar da Mai girma shugaban kasa ya yi na cewar matasa kada su nema a shekarar 2018 kawai abin takaici sai wannan ta zama wata magana ta da ban.

 Gwamnan Kaduna El-rufai ya zo da abubuwan ci gaba wanda a baya mutane suka dinga suka kuma sai gashi yanzu mutanen sun fara fahimta, me zaka ce akan wannan?

Gaskiyar magana ba wai maganar son zuciya ba, mai girma Gwamna El-rufai ya riga ya gama da mu, ala misali maganar na’urar kada kuria’a da gwamnatin sa ta fara amfani da ita a zaben kananan hukumin da aka kammala a jihar ya isa babban misali, kuma su kansu ‘yan adawa sun kasa fitowa su yaba hakan, domin an gudanar da gaskiya da adalci gaskiya take taken na gwamnan akan wannan kawai yasha da mu, haka kuma mai girma gwamnan ya yi amfani da na’urar koda za a zabe shi ko baza a zabe shi ba.

A baya sai dai a shiga daki a rubta abinda ake so amma yanzu a wace wannan.

Baya ga wannan kuma mai girma gwamna ya kirkiro da tsare-tsare da shiye-shiye a cikin shekaru na gwamanatin sa wanda dukkan su sun inganta rayuwar alummar jihar birni da kauye. Kama ta ya yi alummar jihar su biya bashi ta hanyar sake baiwa maio girma gwamna dama a zaben shekarar 2019 don ci gaba da ayyukan ci gaba da ya faro a lunguna da sakuna na jihar baki daya.

Wanne kira zaka yi ga sauran takwarorin sa gwamnoni don suyi koyi dasi wajen yin amfani da wannan na’urar?

Yanzu ba wanda zai yi zabe ya wuce irin na Kaduna sai dai ya kwatanta kamar yadda na ce maka ne yanzu kan dan Nijeriya ya riga ya waye.

 

Advertisement
Click to comment

labarai