Connect with us

LABARAI

An Sasanta Rikicin Kungiyar NUJ Reshen Jihar Kaduna

Published

on


Rikicin da ya dade ana fama da shi a kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Kaduna ya zo karshe a jiya lahadi, in da shugaban kungiyar Kwamared Garba Muhammad ya mika ragamar mulki ga Kwamared Adamu Yusuf don ci gaba da Jan ragamar kungiyar.

Sasancin dai an kwashe kusan shekara daya ana tattaunawa a tsakanin bangarorin guda biyu.

Da yake jawabi wajen mika mulkin, shugaban kungiyar na yanzu, Kwamared Adamu Yusuf ya bayyana jin dadin sa kan wannan sasancin da aka yi. Ya ce wannan ranar farin ciki ne ga kungiyar saboda wannan sasancin da aka yi. Ya gode wa dukkan wadanda suka sanya hannu wajen ganin kungiyar ta ci gaba da tafiya cikin hadin kai da girmama juna.

Kwamared Adamu Yusuf ya yaba wa Kwamared Garba Muhammad saboda hakuri da juriyar da ya nuna tun bayan abin da ya faru a lokacin da aka tsine shi a watan Satumbar 2016. Ya ce yanzu komai ya wuce a kungiyar an dawo da kowa a cikin kungiyar sannan za a ci gaba da tafiya da kowa ba tare da nuna banbanci ba.

A na sa jawabin Tsohon shugaban kungiyar Kwamared Garba Muhammad ya gode wa dukkan wadanda suka taimaka wajen magance matsalar da aka dade ana fama da ita. Ya kira sunayen wasu daga cikin wadanda suka yi kokari wajen ganin an sasanta. Ya gode wa Kwamared Yunusa Makarfi, Kwamared Ibrahim Inuwa Kabiru da kuma Malam Abdullahi Yayandi.

Sauran sun hada da Ibrahim Muhammad, Abdullahi Tumburkai, Idibia Gabriel da kuma sauran mutanen da ya ce ba zai iya kiran sunayen su ba.

Kwamared Garba Muhammad ya yi fatan cewa ba za a sake samun irin wannan matsala ba a kungiyar.

Idan ba a manta ba, Kwamared Garba Muhammad ya maka kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Kaduna a kotu bayan an tsige shi daga kujerarsa ta shugabancin kungiyar alhali yana kasa mai tsarki wajen aikin haji. Shari’ar da aka kwashe sama da shekara daya ana yi a tsakanin bangarorin guda biyu kafin wannan sasancin.

 


Advertisement
Click to comment

labarai