Connect with us

LABARAI

An Hori Jama’a Da Su Ci Gaba Da Aikata Ayyukan Alheri Bayan Watan Ramadan

Published

on


Kamar yadda al’ummar musulmin duniya suka yi amfani da watan azumin Ramadan mai albarka wajen ibada da addu’oi tare da aikata alhairi da taimakon juna da sauran su, an bukaci su siffatu su kuma kasance suna aiwatar irin wadannan aiyukan alhairin bayan wucewar azumin na Ramadan, wannan bayani ya fito ne daga bakin babban limamin masallacin juma’a na Shehu Malam Karami dake Unguwar Kofar Waika dake cikin birnin Kano, Sheikh Abdulwahid Muhammad Nazifi a lokacin da yake hira ga manema labarai a gidansa dake unguwar ta Kofara Waika.

Watan Azumi a cewar Shehin Malamin wata ce mai albarka mai kuma dauke da darussa masu yawan gaske, sannan har ila yau wata ce na tsarkake muminai da kuma Allah ke yi wa bayinsa gafara da kuma koyi ga ma’aikin Allah wajen kyawawan dabi’u.

Saboda haka duk wanda ya samu kansa a watan mai albarka ya zama dole ya gode wa Allah, Sheakh Abdulwahid Muhammad Nazifi, ya ce, ya kamata muyi koyi da annabin Ramaha ba zamu samu tsiraba  sai mun yi koyi da shi.Ya shawarci al’ummar musulmi da cewa, ka da domin watan na Ramadan ta wuce sai kuma mu daina aikata aikin alhairi da muka koya a lokacin watan, kamata ya yi mu rubanya aikin alhairi bayan wucewarta, mu kuma zamanto cikakkun bayan Allah .

Babban limamin masallacin juma’ar ya yi kira da babban murya ga al’ummar musulmi kasar nan da duniya baki daya akan muhimmancin hadin kai da taimakon juna tsakanin al’ummar musulmi domin ahalin yanzu bnabu abin da aka fi bukata irin hadin kai da taimakon juna. Malam Abdulwahid ya ba da misalin yadda wadanda ba musulmai ba suke da hadin kai da taimakon juna tsakanin su .

Daga karshe ya yi addu’ar Allah ya baiwa kasar nan zaman lafiya ya amshi addu’oin da aka egudanarwa awatan mai albarka Da fatan iyayen yara za su kula tare da sanya ido game da atrbiyar yaran su daidai gwargwado, har ila yau su tabbatar suna kai ziyara makarantun su domin sannin halin da suke ciki.

 


Advertisement
Click to comment

labarai