Yadda Malam Wakkala Ya Ziyarci Sansanin ’Yan Gudun Hijirar Mada A Zamfara — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Yadda Malam Wakkala Ya Ziyarci Sansanin ’Yan Gudun Hijirar Mada A Zamfara

Published

on


A ranar 8/6/2018 Mataimakin gwamnan jihar Zamfara Mallam Ibrahim Wakkala Muhammad (Sarkin malaman Gusau) ya kai ziyarar jajantawa ga sansanin ‘yan gudun hijira a garin Mada don ganin halin da suke ciki. Malam Ibrahim Wakkala sarkin malaman Gusau kuma mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya shiga damuwa kwarai da firgici da tausayawa ganin halin da wadannan al’umma take ciki a garin Mada. Bayan ya dawo daga kai wannan ziyara ne ya tattauna da majalisar taro ta jihar Zamfara inda bayan tattaunawar ya yi jawabi mai ratsa zuciya tare da kira ga dukkan wanda nauyin tsaron lafiya da dukiya da mutuncin mutanen Zamfara ya rataya kan sa kan su dubi Allah su sauke nauyin da Allah ya dora musu, Inda yake cewa “ Abubuwan da muka je tare da ku muka ziyarci Madam mun yi shi ne dafatan ku da kanku ku ga halin da al’ummarmu suka shiga ciki lokaci ya yi da ya kamata ya kasancewa cewa za a fadawa duniya da kuma gwamnatin Najeriya gwamnatin tarayya halin da al’ummarmu suke ciki a kauyukanmu ana kai musu hari ana tsoratar da su ana firgitar da su mutanen na tserewa suna dawowa garuruwa. Da muka sami wannan rohoto wajibinmu gwamnati ya gam un kula da abin da duk al’ummarmu suke a cikinsa mu nuna damuwarmu akan damuwarsu wannan shi ne dalilin da ya sa muka je kome dadi kamai daci komai hadari kamai wahala mu je mu isko mutanen nan mu ga halin da suke ciki kuma ba wai mu jajanta ba a’a mu ga hanyoyin da za a bi a ceci rayuwar al’ummar da suka zabe mu kuma Allah zai tambaye mu a ranar tashin alkiyama.

Mun je Mada kun ga yadda mata da yara ke ta kuka halin da suke ciki suna neman agaji suna neman taimako ya zama wajibi mu gayawa muku mu a gwamnatin jiha muna iyakar yinmu kuma za mu ci gaba da iyakar yinmu za mu damu da damuwarsu a halin da suke ciki , Sannan kuma mu yi kira ga gwamnatin tarayya cewa ya zama wajibi su fito su cece mu su ceci al’ummarmu daga wannan hadari da muke a cikinsa sannan mu yi kira ga jami’an tsaro baki dayanssu kan cewa su fito su yi aikinsu sannan su ceci al’ummarmu daga halin da suke ciki. Da muna iya rike makami da mu ne za mu rike makami mu je, doka ba ta yarda mu rike makami ba, ya sanya jami’an tsaron nan muna iyakar yin mu wajen karfafa musu da taimaka musu amma abin nan kullum sai ci gaba yake yi yana tabarbarewa muna da damuwa kwarai da gaske ga wannan. In a hanyar da suke bi ne ya zama wajibi mu yi kira da a dawo a duba hanyoyin da ake bi a samo mana mafita wadda yake al’ummarmu da aka sani da zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo mana a jiharmu. Kuma wannan yasa ya zama cewar mu yi kira ga al’ummarmu mu ci gaba da addu’a duk wanda ke da hannu duk wanda ke taimakawa duk wanda ke cikin irin wannan abu wajen ta’addanci ga al’ummarmu da fiirgita su muna rokon Allah ta’ala ya isar mana gare shi kuma mu ci gaba da addu’a Allah ya yi mana maganinsa. Bayan mun dawo daga wannan ziyara kun ga damuwar da al’umma ke ciki mun sani da dama wadanda abin ya shafa uke cikin damuuwa mu a gare mu muna jin damuwar da ke gare mu na ganin al’ummarmu mu gam un tsamar da ita ya fi damuwarmu na wani jifa ko baci da wani zai yi.Kuma da ikon Allah za mu ci gaba da yin duk abin da ya kamata a kan wannan muna tabbatarwa wadanda abin ya shafa da gwamnati da al’ummar jihar Zamfara gaba daya cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba za mu yi iyakar yinmu ko da abu zai ci rayuwarmu ganin cewamun tsamo al’ummarmu cikin wannan hadari da mummunan hali da suka shiga ciki. Gwamnati bayan dawowarmu mun yi mitin da jami’an tsaro da jami’an gwamnati muka kafa kwamiti ya duba yanayin wurin da suke ciki a duba bukatarsu ta gaggawa da inda za su zauna da abin da ya kamata a taimakamusu haka kuma mun yi da jami’an tsaro su kawo mana abin da keg are su na ganin sun tura jami’an tsaro a dukkan kauyukanmu domin mutanenmu su sami kwanciyar hankali don ganin akwai jami’an tsaro a tare da su. Wannan zai sanya cewa wadanda suka yi gudun hijira suka bar gidajensu za su ami kafa da dama su koma gidajensu don su ci gaba da harkokinsu nay au da gobe. In sha Allahu za mu ci gaba da dukkan abin da muke yi kuma muna kira ga al’ummarmu musamman a cikin watan Ramadan musamman masu tafsirai da malamanmu da limamanmu a ci gaba da addu’a jahar Zamfara mun shiga hali da muke bukatar addu’a mu koma ga Allah subhanahu wata’ala ga halin da muke ciki. In jami’an tsaronmu sun kasa ne wajibi ne mu ma mu nemi mafita ba za mu yi kwance ba mu kyale irin wannan abu yana faruwa ga al’ummarmu mun sani muna sane duk jinin da ya zuba sai Allah ya tambaye mu duk wanda ya firgita sai Allah ya tambaye mu duk wanda ya yi kuka akan yana neman taimako ranar tashin kiyama sai Allah ya tambayi gwamna sai Allah ya taimaki mataimakin gwamna sai Allah ya tambayi kowa daga cikin wadanda mune suka zaba kan halin da muke ciki. Muna rokon Allah ya taimaka mana y aba mu mafita kan halin da muke ciki.”

In dai ba a manta ba jihar zamfara na daya daga cikin jihohin da Allah ya jarrabta da tashe-tashen hankula da rashin tsaro da satar mutane da garkuwa da su da hare-hare ga al’ummar da ba ta jib a ba ta gani ba. Duk kokarin da hukuma ke yi abin na neman cin tura tare da rasa bakin zaren.

 

Advertisement
Click to comment

labarai