Connect with us

LABARAI

Na Koma PDP Ne Saboda Sanata Abdul Ningi –Asabe Turum

Published

on


Shugabar matan Jam’iyyar GPN ta shiyyar arewa maso gabas Hajiya Asabe Isa Turum ta bayyana kudirinta na barin kujerar shugabar mata ta jam’iyyar GPN inda ta koma cikin jam’iyyar PDP wacce a halin yanzu ta kasance jam’iyya mafi karfin adawa a Nijeriya.

Asabe Turum ta bayyana haka ne a jiya cikin wani biki da aka shirya domin karbarta da wasu mutane masu yawa zuwa cikin jam’iyyar ta PDP, inda cikin jawabinta ta bayyana cewa dama sun bar PDP zuwa GPN saboda ubangidan siyasar su Malam Isa Yuguda bayan an fadi zabe, amma daga baya kuma suka lura akwai bukatar a sake tara karfi waje guda domin ceto mutane daga cikin halin da suka shiga na wahala a kasar nan don haka akwai bukatar a samu jarumi irin Sanata Abdul Ningi a Jihar Bauchi don a goya masa baya wajen tsayawa takarar gwamna a Jihar Bauchi, don haka suka sake salon tafiyar don kai wa ga nasarar ceto mutane. Hakan ya sa ta bar Darakta Kamfen ta Malam Isa Yuguda ta kuma bar shugabancin matan jam’iyyar a shiyyar arewa maso gabas don raya wannan tafiyar.

Don haka Hajiya Asabe Turum ta bayyana cewa Malam Isa Yuguda Ubangidan siyasar su ne kuma har kullum suna tare da shi, amma ganin dama daga PDP suka koma GPN kuma yanzu akwai bukatar a samu sabuwar hanyar ceto mutane daga cikin jarrabawar da suka fada a kasar nan. Don haka ita da mutanen ta suka ga bin wannan hanya shi ne mafi alheri don a sake hada karfi a ceto ‘yan Nijeriya ganin yadda jam’iyyar APC mai mulki ta gaza cika wa mutane alkawurran da ta dauka musu game da inganta rayuwa.

Ta bayyana cewa Sanata Abdul Ningi mutum ne wanda ya taka rawar gani wajen ciyar da kasa gaba don haka akwai bukatar a ba shi dama ya jagoranci Jihar Bauchi saboda ganin gudummowar da ya bayar a majalisar wakilai da ta dattijai lokacin da ya wakilci mutanen sa. Asabe Turum ta bayyana cewa ko shakka babu idan ya samu kujerar gwamna za a samu ci gaban da ba a taba samun irin sa ba saboda ganin yadda ya kware a fannin aikin inganta rayuwar mutane a siyasance.

Hajiya Hassana Datti daga Tafawa Balewa ta bayyana cewa ta shiga PDP saboda ganin irin kokarin da ta yi wajen ciyar da mutane gaba a yayin jagorancin su na shekaru 16 don haka ta san akwai masu biyo su daga cikin APC da sauran jam’iyyun siyasa don ganin yadda mutane ke bukatar a ceto su daga cikin halin da suka shiga a siyasance.

Alhaji Ado Yakubu Rahamaniyya shima ya bayyana cewa suna goyon bayan Hajiya Asabe Turum don a gina jam’iyyar PDP kamar yadda a baya ta kasance lokacin da ta ke shugabar mata kuma aka samu ci gaban siyuasar don haka sun ji dadin sauya shekar don a sake gina PDP ta kai ga samun nasara a zabuka masu zuwa.

Alhaji Inuwa Durbin Inkil shima cikin jawabinsa ya bayyan cewa Sanata Abdul Ningi na cikin ‘yan siyasa masu kishi, don haka suke son ganin ya fito ya tsaya takarar gwamna don ciyar da Jihar Bauchi gaba. Saboda haka ya bukaci shugabannin PDP da su kasance sun bar kowa ya zabi wanda ya ke so don a samu nasarar tafiyar kamar yadda aka yi tun farkon kafa jam’iyyar PDP amma daga baya da ayyukan son zuciya suka shigo mutane suka taru suka karya ta aka fadi zabe a shekarar 2015.

Don haka ya bayyana cewa yanzu sun himmatu wajen ganin sun sake gina jam’iyyar ta PDP.

 


Advertisement
Click to comment

labarai