Connect with us

LABARAI

Mace Mai Juna-Biyu Ta Mutu Sakamakon Harbin ’Yan Sanda A Zariya

Published

on


Jami’an tsaro na rundunar ’yan sandan Najeriya sun bude wa wata mota wuta har mace mai juna-biyu da goyon da ta mutu a kan hanyar Zariya zuwa Kaduna.

Binciken da LEADERSHIP A YAU LAHADI ta yi game da lamarin ya nuna cewa a yammacin ranar Alhamis wata mota kirar Gulf ta taso daga Lambar Zango da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya dauke da wasu mutane maza da mata da kananan yara.

A na cikin tafiyarsu ne sai motar jami’an tsaro su ka nemi da motar ta tsaya, don amsa wasu tambayoyi bisa zargin cewa motar na dauke da wani mutum da a ke zargin mai laifi ne, amma sai direba ya ki tsayawa. Hakan ya sa motocin biyu su ka yi ta tsere a kan titin har zuwa birnin Zazzau.

Gab da isowarsu unguwar Kwangila da ke cikin Zariya ne sai jami’an tsaron su ka bude wa motar wuta, inda a ka sami tabbacin mutuwar wata mace guda daya mai dauke da goyon yaro dan kimamin shekaru biyu da kuma tsohon ciki da matar ta ke da shi.

Wakilinmu ya garzaya gidan mamaciyar da ke anguwar Danraka da ke Samaru a karamar hukumar Sabon Garin Zariya don jin ko menene gaskiyar abin da ya faru.

Malama Jummai Danjalo ce mahaifiyar wacce a ka kashe din. Ta tabbatar wa LEADERSHIP A YAU LAHADI rasuwar yarinyar tata mai suna Rabi Abdullahi, wacce su ka tafi taron suna a garin Lambar Zango tare da wasu ’yan uwanta mata.

 

Wakilinmu ya tambayi Malama Jummai ko akwai wani zargi da a ke yiwa su ’yaran nata, sai ta kada baki ta ce, ita dai abin da ta sani a halin yanzu shi ne Rabi da sauran ’yan uwanta sun shiga motar wani da jami’an tsaro ke neman shi ruwa a jallo mai suna Abdullahi Likita. Hakan ya sa jami’an su ka biyo su, daga karshe su ka bude wa motar wuta.

“Ya zuwa yanzu an tabbatar min da cewa ita Rabi ta rasu, akwai mai suna Jummai ita kuma an harbe ta a hannu ta na asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello a Shika da ke Zariya a na duba yanayin jikinta,” in ji mahaifiyar Marigayiya Rabi, wacce kuma ta koka da cewa, har yanzu ba a ba su gawar diyar tasu ba, don su yi ma ta jana’iza.

Ta kara da cewa gawar ta na can babban ofishin ’yan sanda na Zariya, sai ta yi roko da a taimake ta a ba su gawarsu.

LEADERSHIP A YAU LAHADI ta nemi jin ta bakin jimi’in hulda da jama’a na rudunar ’yan sanda na jihar Kaduna, DSP Muktar, don jin ta bakinsu a kan lamarin, amma sai ya ce,

gaskiya ya zuwa yanzu rundunar ’yan sandar ta jihar Kaduna na kokarin samun cikakken bayani a wajen mataimakin kwamishinan ’yan sandar shiyyar Zariyan. Saboda haka bisa dalilan tsaro ba zai yiwu a ce komai ba kan lamarin. Don haka ya tabbatar da cewa da zarar yanayi ya bada dama za su shelantawa duniya halin da a ke ciki.

Ya zuwa yanzu dai jama’a ne ke yin dafifi a gidan mahaifiyar mamaciyar, musamman yadda a ka ce mamaciyar an harbe ta ta na tare da goyon yaro a bayanta tare da tsohon ciki; haihuwa yau ko gobe.

Bugu da kari, rashin cikakken bayani da zai bayyana zargin da a ke yiwa jama’ar da a ka bude wa wuta a motar ya sa jama’a na kishin son jin halin da lamarin ke ciki.

 


Advertisement
Click to comment

labarai