Connect with us

LABARAI

Idan Ba Mu Goge Wa Buhari Ba Mun Yiwa Allah Butulci –Babawo

Published

on


A ci gaba da jin ra’ayoyin al’umar Nijeriya akan zagayowar ranar damakuradiyya da kuma murnar cikar gwamnati APC shekaru Uku da kama ragamar mulki wakilinmu ya sami jin ta bakikin daya daga cikin fitattun yan siyasar jihar Kaduna a karkashin jambiyar APC wato Honorabul Garba Datti Babawo dan majalisar tarayya mai wakitar Sabon Garin Zariya a jihar Kaduna.

Honorabul Garba ya farane da godiya ga Allah madaukakin Sarki da har ya kawosu wannan rana, kuma ya nuna farincikinsa akan yadda ranar ta samesu suna da abin da zasu fada wa al’uma a matsayin samun nasara ga al’umar kasa baki daya .

Honorabul ya fara kawo misalinsa ne da samun nasaran da wannan gwamnati ta samu akan matsalar tsaro da ta samu ya tabaibaye wannan kasar tamu Nijeriya wato maganar Boko Haram wanda yanzu jama’a da yawa suna barci har da masori yace sun godewa Allah akan hakan.

Sannan kuma ya tabbatar da murkushe badakalar cin hanci da rashawa da ya tabaibaye gwamnatin Nijeriya a matsayin bubban nasara a siyasance wanda wajibi ayi jinjina akan wannan lamarin

Ya nuna cewa kowa yasan an sami gagarumar nasara akan harkar noma a fadin kasa baki daya, wanda yace a yanzu kashi 60 cikin 100 na shinkafar da ake amfani da ita a nan gida Nijeriya mu muke nomata banda sauran kayan amfanin gona.

Ya kuma bayyana samun gine-gine a makarantu gwamnati manya da kanana shima dole asashi cikin nasara a wannan lokacin tunda basu a lokacin baya.

Da honorabul ya koma bangare kudancin Nigeriya ya tabbatar ko a baya basu sumi irin aikin da suke samuba a yanzu.

Yace in muka komo arewacin Nijeriya kuwa zamuga tuni shugaban kasa Muhammad Buhari ya bada damar malala hanyoyi tundaga kudu har arewaci kasar don yan Nijeriya su shaida romon damukuradiyya yace ga maganar gina Dam-Dam da zai kankama a arewacin Nigeriya don bunkasa harkar noma da kiwo a wasu muhimman gurare da akaga ya kamata, kuma ya ce tuni maganar gyara hanyar data taso tun daga Kano har Zuwa Kaduna ta wuce Abuja abin yayi nisa.

Kuma don tabbatar da morewa damukuradiyya a wannan gwamnatin shi yasa zakaga an fito da tsaretsaren tallafawa kungiyoyi masu zaman kasu tare da kirkiro dabarun koyawa matasa dogaro da kasu da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi sukeyi yace shima duk nasarace da zasu iya shelantawa duniya a matsayin su na masu son cigaban da ake samu a wannan lokaci.

Karshe ne ya baiyana rashin jin dadinsa game da yadda wasu marasa kishin kasa suke so su dawo da hannun agogo baya ta hanyar wata dabi’a ta yin garkuwa da mutane yace, shima da yardar Allah gwamnati na nan tana duba yadda zatabi don dakile lamarin. Don kuwa tuni wannan gwamnati tayi odar jiragen yaki daga kasar Pakistan banda wanda za suzo daga kasar Amurka don dai karfaf maganar tsaron jama’ar kasa baki daya.


Advertisement
Click to comment

labarai