Connect with us

DAGA NA GABA

Hon. Salisu Isa Dangulbi: Gwarzonmu Na Mako

Published

on


Nagari na kowa ne kalmar da ta dace da Hon. Salisu Isa Dangulbi, shugaban karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, domin mutum ne na mutane wanda ba ya kosawa ko gajiyawa wajen hidimar al’umma. Bayanai sun nuna cewa, kulawarsa da nuna kishinsa ga jama’arsa ya sa al’ummar karamar hukumar mulki ta Maru da Bungudu su ka ga dacewar ya fito, don ya wakilce su a majalisar tarayya.

 

Tarihinka

Sunana Salisu Isa Dangulbi. An haife ni a garin Dangulbi a shekarar 1969. Kamar yadda yake a kasar Hausa an sa ni makarantar allot un ina karami inda daga bisa ni da na dan tasa a ka kaini makarantar firamare ta JNI da ke garin Dangulbi. Bayan na kammala na sami nasarar wucewa makarantar sakandire ta gwamnati da ke Dansadau inda na kammala karatuna na sakandare. Bayan na kammala sai na sami gurbi a college of administration da ke garin Sokoto inda na sami karamar shaida a fannin kananan hukumomi sannan bayan n agama na kuma neman gurbi a wannan makaranta na sami shaidar babbar difloma a dai kan kanann hukumomi.Bayan na kammala na fara aiki da karamar hukumar mulki ta Gusau a 1986 inda na fara aiki a matsayin accountat a karamar hukumar Gusau ina nan na rike mukamai da daman a rike matsayin planning officer na karamar hukumar Gusau na rike internal auditer na rusasshiyar karamar hukumar mulki ta Garaga da kuma karamar hukumar mulki ta Maru sannan ina Hajj registration officer mai kula da karbar kudaden alhazai na karamar hukumar Maru. Daga bisa ni a a 2011 lokacin da aka kada wata gangar siyasa mai zafi wannan ya san a ajiye aikin gwamnati na fada siyasa gadan-gadan. Bayan na shiga siyasa a jam’iyyar ANPP cikin hukuncin Allah aka zabe ni a matsayin sakataren jam’iyya na ANPP na jihar Zamfara. Ina wannan matsayi aka yi gwagwarmaya har muka ci zabe. Muna nan sai aka yi maja aka hada jam’iyyu muka samar da jam’iyyar APC an zabe ni a matsayi sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC da ke jihar Zamfara. Wanda ina cikin wannan matsayi ne mutanen karamar hukumar Mulki ta Maru ta gay a dace da na fito na nemi matsayin zababben shugaban karamar hukumar mulki ta Maru wand anike kansa har zuwa yanzu da nake Magana. Na sami sarautu da dama daga uwayena iyayen kasa daga wannan jihar ta Zamfara da ma wajenta.An ba ni Sarautar Tafidan Dangulbi an ba ni sarautar Mabudin Maru an ba ni sarautar Baradan Dansadau an ba ni sarautar Oba metor na Laji Landa da ke jahar Ondo. Na halarci kwasa-kwasai da dama da tarukan karawa juna sani na sanin makamar aiki kana bin da ya shafi mulki da sha’anin kudi da sauransu. Ina da mata biyu da yara bakwai.

 

Me ya ja hankalinka da har ka ajiye aikin gwamnati ka fada siyasa?

Lokacin ina aikin gwamnati sannan muna bayar da goyon baya ga siyasa musamman ga jagornmu Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura muna tare da shi duk da yake muna ma’aikata. A lokacin ina rejistration officer muna Makka tsohon gwamna na wannan lokacin Mamuda Shinkafi ya koma jam’iyyar PDP bayan mun dawo siyasar ta yi zafi ni kuma akwai yayana Alhaji Lauwali dan Iliya Dangulbi aka bas hi sakataren jam’iyya saboda zafin siyasar a lokacin sai aka bukaci cewa duk wanda ke aikin gwamnati kada ya kuskura a gsn shi gidansa. Ni kuma sai n ace ba za ta yiwu ba da a ce min ba zan je gidansa ba gara na ajiye aikin. Haka kuwa aka yin a dauko fayal dina na rubuta ritaya. Daga nan na fada siyasa.

 

Wane ne ubangidanka a siyasa?

Ubangidana shi ne Maigirma Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Abubakar Yari, Shattiman Mafara, shi ne kuma jagora na a gidan siyasar jihar Zamfara.

 

Ubangidanka ya shekara bakwai ya na mulki. Wanne abu ne ka ke ganin ya yi da ya cancanci yabo a kananan hukumomin da ku ke mulki?

Idan za a ce abubwan da maigirma gwamna ya yi tsahon jagorancinsa a gwamna abin ba zai fadu ba don abin da yawa wai mutuwa ta shiga kasuwa sai dai a takaita. Babban abin da nake alfahari da shi bai fi hanyar da ya sheka mana ba wadda ta tashi daga magami ta je bindin ta je garin da nake Dangulbi har ta zarce zuwa Dankurmi.Wannan hanya mun sha fama da ita tun muna yara muke kokarin mu gay a za a yi ta samu duk tsahn mulkin da aka yi tun muna jihar Sokoto ba a sami yin wannan hanya ba sai a lokacin Honourable Abdul’aziz Yari. Ina alfahari da wannan hanyar wanda ko da ni ne gwamnan jihar Zamfara na cancanci mutanen Dangulbi da duk wanda ke bin wannan hanya ya daga min tuta. A bangaren titian bayan kowacce hedikwata ta karamar hukumar mulki an sada ta da karamar hukumar Gusau sannan kuma kowacce karamar hukumaan bude titinanta an yi kwalta ingantacciya. Ya yi hanya wadda ta tashi daga Anka ta bi daki takwas zuwa Gumi ya yi hanya daga Talatar Mafara zuwa Koloni ta bi ta Rimi hanyar ‘Yar Kokoji ta kule can hanyar Shinkafi. Bayan wannan duk wanda ya dubi hanyar da ya kammala wadda ta tashi daga wanke Bawa ganga Kwanar Ganuwa ta kule Bilbis bayan wannan an yi hanya daga Gumi zuwa Fas zuwa Galange akwai hanya daga ‘Yandoto zuwa Mada. D dai sauransu.

Abin da ya shafi asibiti kuwa mai girma gwwamna ya sami hanyar gyara babban asibitinmu da ke garin Maru an bude shi an sa masa gadaje da kayan aiki haka duk wanda ya dubi asibitin da aka gyar ana na Yariman Bakura Specialist Hospital wanda wannan aibitin zai yi gogayya da duk tsaransa da ke fadin kasar nan .

 

Jihar Zamfara za ta iya gogayya da sauran jihohi kenan?

Wanda duk ya san jihar Zamfara a shekarun baya ya zo jihar Zamfara a yau zai ga abin mamaki na ci gaba. Akwai muaten Zamfar ada suka tafi irin ci ranin nan wajejen Lgos da sauransu suka kwashi shekaru hudu zuwa biyar bas u dawo baa kwai wanda ya zo daga cikinsu garinsu karamar hukumarsu amma ya kasa gane inda gidansu yake domin kwalta ta bi har kofr gidansu duk wanda ya zo jahar Zamfara yasan tana gogayya da tsararta wajen ababen more rayuwa.

 

Batun da a ke yi na jihar ta na cikin jahohi masu talauci, yanzu babu kenan?

Wannan maganar duk masu fadinta bas u san jahar Zamfara ba wasu suna ganin samar da kudin gwamnati shi ne arziki a kasa su a fai-fai kowa ya kwasa a je a yi bushasaha sannan za a ce jaha ta yi arziki amma tsarin shugabanci na maigirma gwamna wanda ya yin a ya gina abin da mu da jikoki da diyan diya za mu mora mu yi bugun gaba da alfahari da shi ko maganar nan da muke jihar Zamfara bara ta noma abincin da ya na kusan ciyar da arewacin Najeriya. Sabode haka maganar yunwa da talauci a jahar Zamfara bai taso ba.

 

Zaben shuwagabannin jam’iyya da a ka yi, ya ka ke ganin haskensa a babban zabe da ke zuwa?

Alhamdulillahi zabe kam musamman na jahar Zamfara an yi shi cikin adalci wanda har aka yi shi aka gam aba a sami wani korafi ba ko fada. Zaben ma da aka yin a shugabannin APC na jaha duk a na tare gwamna da mataimakin gwamna suna wajen, ’yan majalisunmu su 24 su na wajen shugabannin kanann hukumomi su na wajen guda 14, ’yan majalisar tarayyarmu su na wajen sanatocinmu duk su na wajen banda mutum guda shi ne bai sami zuwa ba, don ya na da dalilinsa na kashin kai, ba wanda ya shafi al’umma ba.

 

Me ya hana shi zuwa kenan?

Jihar Zamfara tun da mu ka tashi kanmu a hade ne tun lokacin da Mai girma Yariman Zamfara Alhaji Ahmad Sani ke mulki har zuwa yau a na zabe ne bisa ga cancanta ta mutum da ganin ya na iyawa shuwagabanni su ce shi zai yi. Shi kansa wanda ya ke jayayyar da zai tambayi kansa yaya ya zo inda ya ke. Lokacin da muke wannan tafiyar ya shigo jam’iyya mu na da ’yan takara, amma saboda ladabi da biyayya na shugabanninmu aka dakatar da wani daga takarar aka ce a ba shi kuma hakan aka yi aka kuma yi masa duk abin da ya dace a yi masa kuma ya ci zabe. To ashe yanzu don za ta je ga wani bai kamata mutum ya budi baki har ya kalubalanci abin ba. Inda aka ce cikin mutu dari duk suka amince sai goma suka kabalanci abin ai duk iyakar nasara an same ta. Da ma ba yadda za a yi a yi abu dari bisa dari a goyi baya sai dai a’ala a sami rinjaye. Mu muatnen Zamfara ladabinmu da biyayyarmu da wulayarmu suna nan daram!

 

Jihar Zamfara na fama da tashe-tashen hankula. Wanne kokari ku ke yi a matsayinku na shugabannin kananan hukumomi?

To kamar yadda ake ji kuma ake gani a kafafan yada labarai jihar Zamara na daya daga cikin jihohin da ke fama da wannan tashe-tshen hankula Allah ya jarabce mu da al’amari na tsaro amma al’amarin tsaro al’amari ne na duniya (global issue) ba ma Najeriya ba.Jihar zamfara na ciki musamman abin da ya shafi satar shanu garkuwa da mutane satar mutane da ma farwa wadanda bas u jib a bas u gani ba a ka she su. Amma gwamnati na iyakar yenta domin ta ga an sawo kan wannan al’amari. Matsalar tsaro ta zama kamar rigar siliki kana janyo nan can na zillewa saboda sulbinta. Ana kasha makudan kudi daga gwamnati maigirma gwamna ya sai mota hilud sama da dari an rarrabata ga jami’an tsaro domin su shiga sako da lungu don su taimaka wajen wannan dakile wannan rashin tsaron. Maigirma gwamna ya kasha kudi sama da biliyan Goma sha biyar wajen al’amarin tsaro tun daga alawus na jami’an tsaro da tallafin da kae bayarwa ga wadanda ibtila’in ya fadawa wadanda suka rasa ‘yan’uwansu ko wadanda aka jikkita. Da abincin da ke saya na jami’an tsaron da sauransu. Su ma shugabannin kananan hukumomi ba su rungume hannunsu ba, su na iyakar yinsu domin su ga sun taimakawa yunkurin gwamnati.

 

’Yan uwanka ciyamomi na wasu jihohi na kuka da sabon tsarin komai sai dai gwamna ya yi. Ku ma ku na da wannan korafin?

Mu kam a jihar Zamfara babu abin da za mu ce sai Alhamdulillahi domin kason da muke samu na kudade daga baitul malin kasa wanda ake rabawa zuwa ga jihohi da kananan hukumomi ana aiki da kason ta hanyar da ya dace. A wannan bangare muna dagawa gwamna tuta akwai lokacin da ake ta surutun ya kamata mu sami anatomy a kasha join account wanda ni nake cewa a nawa ra’ayin ba da yawun kowa ba ni a ganina idan dai yadda maigirma gwamna ke gudanar da join account a jahar azamfara haka za a ci gaba da yi to ni ina goyon bayan a ci gaba da barinmu a join account. Wanda nake na bayar da alilai nid an jihar Zamfara ne kuma a cikinta nake zaune. Tun 1999 da aka buga kugen siyasa an yi lokacin da ana bawwa ciyamomi autonomy din kan lokaci, amma ba su iya yin aikin da ya tashi daga magami zuwa Dangulbi ba titin da mai girma gwamna ya yi mana a yanzu ba a iya aikin da duk maigirma gwamna ya yi ba. Amma yanzu da join account din duk maigirma gwamna ya yi wadannan dinbin ayyukan wanda hadin gwiwa ne da abin da yake samu shi a matakin jiha da mu abin da muke samu a matakin kananan hukumomi sai a hada domin a ga an yi wani aiki da za a gani a karamar hukumar da aka dauki kudinta.

 

Akwai hotuna da a ke ta yadawa na rokon ka fito takarar dan majalisar tarayya. Za ka cikawa masu wannan fatan buri?

Kamar yadda ki ka sani an ce mai rai bay a rasa motsi. A lokacin da nake rike da mukamin sakataren tsare-tsare na jam’iyya na Zamfara mutane ne suka jawo ni na cewa na zo na yi musu takarar shugaban karamar hukumar mulki ta Maru a lokacin na fada musu nib a zan amsa musu ba sai nag a maigirma gwamna y aba ni dama. Bayan nag a maigirma gwamna y aba ni daman a na fito na nemi wannan matsayi kuma cikin yardarm Allah na fito kuma aka yi muwafaka na sami wannan dama. To ko a yanzu ‘yar gidan jiya ce da siyasa ta da wulaya ta da biyayyata suna ga maigirma gwamna Honourable Dr Abdu’aziz Yari Shatiman Mafara b azan yi riga malam masallaci ba. Na fadawa masu fatan alheri a ko’ina daga Maru da Bungudu cewa nema wajibi ne a nema amma bayarwa tana wajen Allah b azan so na amsa ba don ban san uzirin maigirma gwamna ba da wadanda ke da ruwa da tsaki cikin wannan al’amarin ban a siyasa. Har yanzu idan maigirma gwamna lebura y ace na zo na yi shi zan yi idan ma y ace chairman ka tsaya ba z aka yi takara ba wannan lokaci nawa sami’ina ne wa a da a na. Maganar takarar danmajalisa ba wai takara ce ta a mutu ko a yi rai ba amma masu yi ma fatan alheri ba z aka ce su bari ba muna nan tare da su idan haka Allah ya kaddara za a yi haka nan za a yi za mu ba su kyakkyawan jagoranci bisa abun da suke zato da tuhuma gare mu iyakar kokarina domin nag a an ba marar da kunya.

 

Wanne kira gare ka ga takwarorinka ciyamomi don gani kun inganta jihaar Zamfara?

Ciyamomin jihar Zamfara dukkanmu muna da alkibla guda it ace ta samar da ababen more rayuwa da samar da ingantattan turba ta biyayya da da’a. Don haka kira na da zan kara gare su shi ne na mu kara hada kanmu mu gam un taimakawa maigirma gwamna Dr Abdul’aziz Yari ya isa inda yake son ya isa kuma muna yi masa fatan alheri dai-daikunmu da a gamenmu muna yi masa fatan alheri a dukinda ya sag aba.Kuma ciyamomi in aba ki tabbacin shi maigirma gwamna a duk inda ya dauke kafa zai ga ciyamomin jihar Zamfara saboda karamci da diyauci da mutumtawa wadda ya yi zuwa ga shuwagabannin kanann hukumomi da dimbin ayyuka da ya baza a kananan hukumomi.

 

Wanne kalbale ka fuskanta tun daga lokacin da ka shiga siyasa?

Kalubalen da na fuskanta yanzu duk sun wuce musamman 2011 lokacin da muka fara siyasar adawa lokacin ba mu da gwamnati shi wanda muka zaba a jam’iyyar ANPP ya kwashe kayansa ya koma jam’iyyar PDP kuma ya tafi da ciyamomi da kwamishinoni da masu ba wa gwamna shawara tare da wa da wa…. Allah da ikonsa sai ya barmu da maigirma sanata Ahamad Sani Yariman Bkura da shi maigirma gwamna mai ci yanzu haka muka yi ta gwagwarmayar mun sami kalubale na shari’a na a kama mu a kai mu ofishin ‘yan sanda na kama mu a kai mu gidan yari na kamamu ba wani tashin hankali da ba mu gani ba a cikin gwagwarmayar mun gudu mun bar gidajenm ba mu Abuja ba mu Kano ba mu Lagos saboda mu tsita da mutuncinmu ga wadanda suke son su ci mana mutunci.amma cikin cewar Allah da ikonsa aka zo zabe maigirma gwamna ya lashe zabe Allah ya mayar da wannan mulki ga wannan jam’iyya. Mu jihar Zamfara PDP ba ta taba cin zabe ba kuma ba za ta ci zabe ba in Allah ya yarda domin za mu fito mu kare nasarar da muke samu ala kulli halin. Alhamdulillah wannan duk ta wuce da ma duk gida guda muke su kansu wadanda muka yi gwagwarmayar da su da mu kanmu an sake dawowa an hade an yafewa juna bisa ga abubuwan da suka gabata. Hatta maigirma gwamna ya ja wasu daga ciki y aba su mukamai a gwamnatinsa. Zamfara da ma dangi ne burin kowa shi ne ciyar da jahar a gaba.

 

Wanne kira za ka yi wa al’ummar karamar hukumar Maru?

Mutanen jihar Zamfara a siyasance alkiblarsu guda mutanenmu na karamar hukumar mulki ta Maru alkiblarsu guda kirana gare su shi ne mu kara hada kanmu don mu ba wa maigirma gwamna damar ya karasa sauran ragowar zangon da ya rage masa lafiya mu roka masa Allah y aba shi kyakkyawan mafita ga inda ya sa gaba.

 

Akwai rashin ayyukan yi ga matasa wanda shi ke haifar da wasu ayyuka na laifi a kasa. Wanne mataki ku ke dauka a jihar Zamfara?

Gaskiya a jahar Zamfara lokacin da maigirma gwamna ya ci gwamna mun isko irin wannan matsalolin na matasa babu aikin yi amma sai aka fito da wani tsari inda ya sa a samar da wasu kamfanoni guda biyar aka yi masa rijista y aba da dama kowane kamfani a yi masa rigista kuma y aba da dama kowanne kamfani ya dau matashi sama da dubu aka bas u aiki na clearance na gari wanda duk wata akwai alawus da ake biya zuwa ga wannan kamfani. Kinga an dauki matasa sama da dubu biyar wannan ba karamin al’amari ba ne an rage yawan matasa masu zaman kashe wando. Wannan bayan wadanda ake dauka a guraben ayyuka hatta kananan hukumomi akwai tsari da za dau matasa wadanda za su ci gaba da kula da hedikwatocin kananan hukumomi.

 

Mene ne burinka?

Mai rai ba ya rasa buri da ma buri yake mutuwa tunda mun tsincikanmu cikin siyasa muna da burace-burace amma kana taka Allah na tasa ne amma saboda cikakkar biyayyar da nake da ita ga maigirma gwamna idan ina da burin na cimma abu fari in jagorana ya ga ruwan bula ya fi dacewa da ni to a shirye nake na sa hannu bibbiyu na karba tare da godiya ga Allah.


Advertisement
Click to comment

labarai