An Kashe Miliyan 28 A ‘Juyin Sarauta’ Amma Ganduje Bai Taimake Mu Ba –Ramat — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

BIDIYO

An Kashe Miliyan 28 A ‘Juyin Sarauta’ Amma Ganduje Bai Taimake Mu Ba –Ramat

Published

on


Fim din Juyin Sarauta, wanda fitacciyar marubuciya kuma furodusa, BALARABA RAMAT YAKUB, ta dauki nauyi ya zama zakaran gwaji tun gabanin fitowarsa a kasuwa, inda ya ke ta lashe kambu a duk gasar da a ka shiga da shi. Ya zama gwarzon fim na yarukan cikin gida a Najeriya a gasar Zuma Film Festibal Awards da a ka gudanar watannin baya, wato Best Indigenous Language Film’, inda ya bai wa finafinan Yarabanci da na Ibo kashi a gasar. Bugu da kari, ya samu fitowa a manyan rukunan gasa guda 14 na AMMA Awards Season 5 da a ka gudanar kwanakin baya, inda ya lashe guda shida daga ciki, wadanda su ka hada da Gwarzon Jarumi wanda Ado Ahmad Gidan Dabino ya lashe, Gwarzon Kirkirarren Labari wanda Balaraba Ramat Yakub ta lashe, Gwarzon Mai Daukar Hoto wanda Nasiru Dorayi ya lashe, Gwarzon Tsara Dandali wanda Aliyu Shehu Yakasai da Abubakar S. Reshe su ka lashe. Sai kuma Gwarzon Kidan Taushi wanda Habibu Lafazi da Ibrahim Danko su ka lashe, sannan Gwarzon Siddabaru wanda Ali Musa Danjalo da Faruk Sayyadi su ka lashe. Haka nan sauran guraben da ya samu fitowa (nominations) sun hada da Gwarazan Kwalliya, Sauti, Sutura, Hada Hoto, Mataimakin Jarumi, Mataimakiyar Jaruma, sai kuma Gwarzon Fim da Gwarzon Darakta. Ganin irin wannan gagarumar nasara da Juyin Saraura ke samu, Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya tuntubi Hajiya Balaraba Ramat, don jin sirrin boyen. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Ko za ki iya gaya wa masu karatu abinda labarin Juyin Sarauta ya kunsa a takaice?

Labarin fim din an gina shi ne kan Sarauta da yadda matan sarakai da kwarakwaransu su ke juya akalar kowane irin abu a farfajiyar gidan sarakai. Sau tari za ka ka ga har warware abin da a ka zartar a fada su ke yi kuma su aiwatar da nasu, kuma dole a tafi a haka ko da sanin sarakunan ko kuma babu saninsu.

 

Me ya dauki hankalinki ki ka zabi labarin Juyin Sarauta a matsayin wanda za ki shirya?

Labari ne na mulki irin na mata, inda kowacce ta gwada isarta da iya mulkinta tare da iya shiga da fita a gurin bokaye da malamai da kuma ‘yan tsubbu. Wannan ne ya ja hankalina, domin saurata ta mai rabo ce kuma ba a sarki biyu a gari daya. Ko masu nema sun kai dari, to dai daya ne zai hau.

 

Da alama an kashe makudan kudi wajen shirya shi. Shin ina ki ka samo irin wannan kudi haka a lokacin da a ke tsoron kashe wa finafinai kudi, saboda faduwar kasuwa?

Gaskiya shirin ya lashe kudi masu yawan gaske. Ma’aikatar kudi ta tarayya ta ba mu tallafin Naira miliyan bakwai. Mun ranto miliyan takwas da dubu dari biyar a gurin banki kasuwanci, sannan kamfanin Ramat Production Limited da Dogarai Kuarters Women su ma sun zuba kudade da yawa a ciki.

 

Nawa a ka kashe zuwa yanzu?

Mu na hasahen wajen miliyan ashirin da takwas ta dulmiya.

 

Ta ya ya za ki mayar da kudinki har ki ci riba?

Lokacin da na shirya fin din Wata Shari’ar Sai A Lahira na ranto kudi daga Bank of the North a wancan lokaci, da na gama fim din sai da na kusan hada uwar kudi da riba a sinema sannan na kai shi kasuwa. Shi ma haka za mu yi wa Juyin Sarauta, duk da dai yanzu sinimu sun mutu.

 

Ganin yadda Juyin Sarauta ke kwashe ‘awards’, mene ne sirrin fim din?

Sirrin dai bai wuce kyawun aikin da a ka yi wa fim din ba. Ma’aikatan kowa ya yi aikinsa tsakani da Allah.

 

Me ya sa ba ki saka daya daga jaruman da a ke yayi ba, ki ka dauko Gidan Dabino?

Ba mu dauko manyan ‘yan wasanmu ba domin dalili biyu. Na farko, mu na son masu kallo su gane labarin da al’adar da ke ciki ba tare da la’akari da fuska ko daukakar dan wasan ba? Na biyu, mu na son a daina zabar dan wasa don kawai ya na da ubangida a masana’antar. Mu kamfaninmu na kowa da kowa ne, idan dai ka cancanta. Sai da mu ka zaga kungiyoyin ‘yan wasa har bakwai mu ka zabo ‘yan wasan da su ka cancanta wajen su 80.

 

Shin me za ki ce game da yadda Gidan Dabino ya buge fitattun jarumai masu tashe ya lashe kambun babban gwarzon jarumi na AMMA Awards Season 5 da fim din Juyin Sarauta?

Ba Ado Ahmad Gidan Dabino MON ne mu ka zaba da fari ba, amma wanda mu ka zaba sai ya kasa a ranar farkon da a ka dasa kyamara. Dole ce ta sa Ado Ahmad ya hau, don ba yadda za mu yi. Aiki ya yi ma sa yawa, amma duk da haka mu ka tilasta shi ya karba. Kuma Allah Ya taimake mu ga shi ya yi, kuma ya isar da sakon fiye da na kowa. Ga shi ya sami ‘nomination’ na Best African Actor Zuma Award 2017 da Best Actor in Leading Role AMMA AWARD 2018, wanda ya lashe. Alhamdulillahi a fim din Juyin Sarauta zaben sarkinmu ba mu yi zaben tumun dare ba. Babu mamaki da hukuncin Allah. Karin magana daya ce a nan; da tsohuwar zuma a ke magani. Tsoho ya daka wa yara kashi ya amshe kambin da kowa ya ke hari kuma ya ke nema, wato Jarumin Jarumai. Mu na kara yi wa Allah godiya kuma mu na kara alfahari da ya ba mu ikon saka ‘MON’ ya hau wannan mataki a fim din Juyin Sarauta.

 

Da yawan ‘yan fim na tsammanin cewa za ki bada aikin bada umarnin Juyin Sarauta ne ga daya daga cikin tsofaffin daraktoci, kamar irinsu Bala Anas Babinlata, amma sai ki ka bai wa Falalu Dorayi, wanda ya na cikin sababbin jini. Shin meye dalili?

Dukkaninmu tsofaffi a wannan tafiya ta Kannywood a na kiran mu ne da suna daya, watau ‘Diddigar Kaya’. Rashin saka daya daga cikinmu ba ya nuna ba mu iya ba ko ba za mu iya ba. Labarin bai gama haduwa ba sai da saka hannun Bala Anas. Idan fim din ya fito ka duba za ka ga Bala ne shugaban wadanda su ka zauna su ka kalkale labarin, kuma bayan zaman tarayyar da su ka yi sai da mu ka kuma zama na musamman ni da shi kafin mu yarda da cewa labarin zai kai labari. Masu ba da umarni da yawa a wannan masana’anta kuma sun san aikinsu da yaran da kuma tsofaffin. Na yi finafinai uku; Wata Shari’ar Sai A Lahira, Tijjani Ibrahim Allah Ya ji kan sa shi ne ya bayar da umarni; Ina Son Sa Haka, Ishak Sidi Ishak ne ya bayar da umarni, sai kuma Juyin Sarauta, wanda Falalu A. Dorayi ya bayar da umarni. Watakila na gaba ni zan ba da umarni ko na nemo mace ta ba da umarni. Allah Ya ba mu sa’a. Amin.

 

Ya ya ki ke ji a ranki ganin yadda fim din ya ke kwashe ‘awards’?

Sai godiyar Allah, alhamdulillahi. Na ji dadi kuma Ina alfahari da wannan ‘awards’ da fim din ya ke samu, domin wannan ne zai nuna ma ka ba wasa mu ka yi ba. Ba daki mu ka shiga mu ka rubuta ba, bincike mu ka yi. Wannan zai nuna ma ka cewa mu na da labarai na al’ada, wadanda za su karbu a duniya. Ba sai mun aro al’adun wasu ba. Ba sai mun gurbata tamu al’adar ba.

 

Yaushe Juyin Sarauta zai fito kasuwa?

Insha Allah Juyin Sarauta zai fito kasuwa, amma ba yanzu ba. Kamar yadda mu ka narka wannan kudi mai yawa, to za mu yi yawo da shi a sinemu ba na gida Najeriya kadai ba, ko a wacce kasa a duniya, indai za su yarda, to za mu je mu nuna shi ko da a birnin Sin ne.

 

Mene ne burinki a kan fim din Juyin Sarauta?

Alhamdulillahi burina bai wuce fim din Juyin Saruta ya zama zakaran gwajin dafi a finafinan Hausa ba. Ina son ya zama matattarar nazari ga yaranmu ‘yan makaranta masu nazari. Kuma Ina rokon Allah Ya sa kudin da a ka yi shi ya dawo tare da gwaggwabar riba, amin.

 

Wane kira ki ke da shi ga sauran masu shirya finafinai da kuma gwamnati?

To, kirana ga masu shirya finafinai ‘yan uwana bai wuce na mu hada kai ba, sannan duk lokacin da za mu shirya fim, tun daga labari mu daure mu dinga tantancewa, domin kyawawan al’adunmu da kuma uwa uba addininmu su ne za su nuna wa duniya ko mu su wane ne. Ta fuskae gwamnati kuwa, ni babu abin da zan cewa Gwamnatin Tarayya sai godiya, domin su ne su ka yi min shimfida, wacce ita ce dan-bar shiga aikin fim din gadan-gadan. Amma a gaskiya gwamnatin Kano ba ta taimake ni da komai ba. Na yi kokari iyakar kokarina na ga sun yaba da abin da na yi, amma babu wanda ya kula ni. Kafin na fara sai da na nemi ganin Mai girma Gwamna Ganduje a ka ce na rubuto takarda. Na aika takarda, amma shiru babu wanda ya yi min magana. Lokacin da na samu ‘Award’ na ‘Best Nigerian Language Film’, Ina murna na tura wa Mai girma Gwamna da takarda, shi ma babu wanda ya amsa ni. Sai mu ka zo za mu yi ‘launching’ din fim din. A nan ma na kai takardar sanarwa, bayan ita na kai katin gayyata hade da littafin shirye-shirye. Mai girma Gwamna bai zo ba, bai kuma turo bai turo ba. Babban darakta na hukumar tace finafinai da dab’i na jihar Kano Malam Afaka shi ya zo; da ya ke mun gayyace shi. Duniya ba ni da garin da ya fi Kano kuma wallahi babu gwamnan da ya fi min Mai Girma Abdullahi Umar Ganduje (Khadimul Islam), amma har yau babu wanda ya saurare ni. Don ni ba ‘yar siyasa ba ce shi ya sa gwamnana ya yi watsi da ni. Na dauka shugaba ya na rike masoyi komai kankantarsa. A gaskiya soyayyata ga gwamna ba ta tsamo ni daga kwata ba.

 

To, mun gode.

Na gode kwarai, Allah Ya taimake mu, Allah Ya ba mu sa’a.

Advertisement
Click to comment

labarai