An Kammala Taron Bita Don Yara Mata 100 Na Kungiyar G4G Da Unicef A Bauchi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

An Kammala Taron Bita Don Yara Mata 100 Na Kungiyar G4G Da Unicef A Bauchi

Published

on


jardawaAn kawo karshen taron bita na mako guda da kungiyar UNICEF tare da hadin guiwar kungiyar inganta rayuwar mata da matasa ta FWOYDI, wato FAHIMTA da taimakon hukumar ilmi ta Jihar Bauchi SUBEB, wanda aka shirya wa yara ‘yan mata guda 100 daga yankunanan karkara wanda aka gudanar da shi a Zaranda Otel da ke Bauchi.

Taron ya kasance karo na biyu inda aka gayyaci yara mata 100 daga kananan hukumomi uku wato Toro da Ningi da Zaki yadda aka tsugunar da yaran aka horas da su dabarun girke girke da sana’o’i na dogaro da kai da kuma karatun boko da na addini da ilmin shugabanci. Bayan haka an ilmantar da yaran yadda za su kasance masu hazaka da sanin yadda zasu zauna da mutane da kuma kare kan su daga mazajen zamani masu lalata tarbiyyar yara ta hanyar gurbata musu rayuwa ko yi musu fyade da makamantan su.

Hajiya Maryam Garba shugabar kungiyar FAHIMTA mai rajin taimakawa mata da matasa ita ne ta jagoranci lura da yara matan da kuma gudanar da aikace aikace yayin taron bitar, ta bayyana wa wakilin mu cewa sun koya wa ‘yan matan sana’o’i kusan guda goma wanda suka kunshi yin kayan sha da kayan abinci da kek da cincin da kayan adon mata da yin takalma da kayan tsabtar gida da sauran su. Don haka ta bayyana cewa a lokacin da yaran suka zo a ranar farko sun natsu sun kuma koyi abubuwan da aka koya musu yadda har sun saba kamar ba za su koma gidajen su ba saboda yadda suka saki jikin su.

Hajiya maryam Garba ta bayyana cewa makasudin shirya taron bitar shi ne don a ilmantar da ‘yan mata ilmin zamani da kuma shugabanci a gida saboda mata sune kan gaba wajen bayar da tarbiyya idan sun lalace mutane da yawa za su lalace musamman kananan yara don haka ta bayyana cewa bayan kammala taron bitar za su yi ta bin su har garurwan da suka dauko su don su ga irin abin da su ke yi na koyar da yara ‘yan uwan su a garuruwan su don su samu ilmin da su zai amfane su. Ta bayyana cewa an gayyato yaran daga kananan hukumomi shida Toro da Ningi da Zaki a baya kuma an gudanar da irin wannan ga kananan hukumomin Shira da Alkaleri da Ganjuwa.

Rakiya Babayo daga karamar hukumar Zaki ita ce ta jagoranci yaran a matsayin shugabar aji inda cikin hirarta da wakilin mu ta bayyana cewa ta fahimci abubuwa da dama a wajen taron bitar saboda ta koyi yadda za ta kare kanta daga wanda zai cutar da ita musamman mazaje saboda yadda cin zarafin mata ya yi yawa daga wasu mazaje masu bata ‘yan mata ta hanyar lalata su da gurbata musu tarbiyya da kuma yaudara ko yi musu fade. Don haka ta bayyana cewa abin da suka koya a yanzu zai taimake su idan sun girma sun yi karatu sun kama aiki ko sun kasance masu iyalai.

Madam Ebere Onyemaechi mataimakiyar shugabar taron kuma jagorar wata kungiya daga Abuja ta bayyana cewa ta zo Bauchi don gudanar da wannan taron bita game da yadda ake ilmantar da yara ilmin zama da iyali da kuma jama’a. Don haka ta bayyana cewa wannan shiri ne da ya kunshi ilmantar da yara mata tun daga makarantun firamare har zuwa sakandare saboda a magance wasu kalubale na gurbatar tarbiyya wanda ke faruwa a wannan zamani.

Ebere Onyemaechi ta kara da cewa wannan aiki ne mai kyau da gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kan su ya kamata su yi koyi da wannan kudiri na zakulo yara mazauna karkara don suma su san ana damawa da su a fannin gudanar da rayuwar yau da kullum ta hanyar ilmantar da su yadda za su kare kan su daga sharrin miyagun mutane a wannan zamani, musamman wadanda ke da mummunar manufa a zukatan su game da yara mata.

Haka kuma akwai bukatar yara tun suna kanana su koyi yadda za su dogara da kan su cikin sauki da tarbiyya ta hanyar sanin yadda za su yi sana’o’i irin na gida don su amfanar da kan su da iyalan su.

Advertisement
Click to comment

labarai