Connect with us

LABARAI

Shugaban NDDC Ya Bukaci Sarakunan Gargajiya Su Wanzar Da Zaman Lafiya A Neja Delta

Published

on


Manajan Gudanarwa na hukumar inganta yankin Neja Delta (NDDC), Dakta Nsima Ekere, ya kalubanlanci Sarakunan Gargajiya da su yi duk mai iyuwa wajen inganta harkar zaman lafiya, tsaro da kuma fitar da ci gaba wa ‘yankin Neja Delta ta fuskacin kokarinsu.

Dakta Ekere wanda yake jawabi a jiya a lokacin da masu rike da sarautun gargajiya ta  TROMPCON, suka kai masa ziyara a shalkwatar hukumar NDDC da ke garin Fatakwal.

Babban jami’in gudanarwa na NDDC ya nemi masu rike da sarautun da su hanzarta sauya kalamansu zuwa ga wadanda za su karfafi zaman lafiya da tsaro a cikin al’ummomiminsu domin samun nasarar isa mataki na gaba cikin kwanciyar hankali Sannan kuma ya ci gaba da cewa, in ba zaman lafiya, babu inda za su iya kai yankinsu.

 

Ya ce; “Hakki ne a kanku, kuma aikinku ne ku saita ‘yan siyasa bisa turbar demokaradiyya wadda za mu ci moriyar wannan demokaradiyyar a yau, kuma al’umma ta gaba wato ‘ya’yanmu da jikokinmu su mora,” in ji shi.

Ya ce, akwai gayar muhimmaci a hada kai wuri guda domin kare martabar demokaradiyya, yana mai shaida musu cewar suna da ta yi wajen nuna wa jama’a shugaban da ya dace a zave shi domin kuma wadanda ba su kamata ba, domin ta haka ne za su taimaki jama’ansu.

Sai ya shawarce su da cewa, a kowane lokaci suke yin nasu kokarin wajen dora ‘yan siyasa kan turba domin kada su mance da muradin jama’an da suke zave, yana mai nemansu da su yi aiki don al’ummar gobe.

A nasa jawabin shugaban masu rike da sarautun na kasa (TROMPCON) Owong (Dr) Effiong Archianga, ya gode wa hukumar ci gaban yankin Neja Delta (NDDC) a bisa samun nasarar cim ma dimbin nasarorin da suka hada da shimfida titi, da sauran ayyukan ci gaba da suka samar, hade kuma da samar da wasu kamfanonin mai har guda 9 da sauran ayyukan da ke daukaka darajar yankin Neja Delta da al’ummarta.

Ya kuma amshi shawarwarin da shugaban gudanarwar ya ba su, yana mai shaida cewar a tasu fannin za su ci gaba da taka rawar da ta dace domin ‘yan baya su mori tsari mai inganci.


Advertisement
Click to comment

labarai