NAERLS Ta Kawo Wa Manoma Mashinan Aikin Gona Ma Fi Sauki — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

NAERLS Ta Kawo Wa Manoma Mashinan Aikin Gona Ma Fi Sauki

Published

on


A makon da ya gabata Cibiyar bincike da wayar da kan manoma da bayar da dabarun noma ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya NAERLS tare da hadin gwiwar ABUCOS sun gudanar da taron kara wa juna sani da nunawa kugiyoyin manoma 50 da suka fito da bangarori daban-daban mashinan aikin gona na zamani da zai rage wahalhalun da ake fuskanta a wajen aikin gona.

Shugaban sashin wayar da kan manoma da bayar da barun noma Malam Murtaka Galadima, ne ya shugabanci taron.

A jawabinsa shugaban ya ce cibiyar ta kawo wannan mashina ne ga kungiyoyin manoman don kawo ci gaban harkar noma a fadin kasa baki daya kuma ya ce, wannan hobbasa, hadin gwiwa ne tsakanin cibiyar da kamfanin ABUCOS.

Kuma ya tabbatar wa da manoma da cewa, mashinan za su taimaka wa manoma sosai tare da kawo ci gaban noma kuma za su bai wa manoman damar mallakar mashina cikin sauki.

Shi ma mataimakin shugaban wannan cibiyar Farfesa Ikanu Emmaniwel, da ya wakilci shugaban shugan cibiyar ya bayyanawa manema labarai cewa, mashinan noma da cibiyar ta kawo nasara ce.

 

Madam Asibi, daya daga cikin manoman mata da suka halarci taron ta fara da godiya ga Allah da ya sa suka zama manoma a wannan kasar kuma ta kara da cewa in Allah ya so za su jarraba wadannan mashinan su gani don ga dukkan alama wahalar da suka sha a baya to a yanzu  komai zai wuce tunda ga shi an zo masu da injin casa shinkafa ga na yin dashenta gana yankanta duk a karamin lokaci zai yi maka aiki mai yawan gaske.

Malam Muhammad shi ma wakilin wata kungiya ce daga karamar hukumar Giwa jihar Kaduna ya ce tuni sun shirya tsaf don karbar wannan tsari kuma sunyi matukar farin ciki da samunsa.

Daga cikin mashinan da cibiyar ta kawo akwai inji noma da huda da na casar shinkafa da na masara da dai sauransu.

Advertisement
Click to comment

labarai