Connect with us

LABARAI

Na Yi Mamaki Da Hamid Ali Ya Kasa Dawo Da Ni Bakin Aikina –Bello Gusau

Published

on


“Na yi mamaki da Shugaban Hukumar Kwastam na kasa, Hamid Ali ya kasa dawo da ni bakin aikina duk da umurnin yin hakan da Kotun Koli ta bayar tun ranar 07/04/2017.”

Tsohon Shugaban Hukumar Kwastam shiyyar Abuja, Alhaji Bello Abubakar Gusau ne ya yi wannan zargin a lokacin da yake zantawa da Wakilinmu, inda ce an kore shi daga aiki ne ba bisa ka’ida ba shekaru takwas da suka gabata, bayan ya gano wata cuwa-cuwa da ake tafkawa a ofishin shiyya na Hukumar da ke Apapa Lagos.

Ya kara cewa bayan an kore shi daga aiki ne ya garzaya babbar kotun Tarayya da ke Abuja, inda ya kalubanci rage masa matsayi da kuma korarsa daga aiki da aka yi ba bisa ka’ida ba, amma sai ya sha kaye a kotun.

Ganin bai yi nasara a nan ba, sai ya daukaka kara zuwa kotun gaba, inda ta bayar da umurnin a mayar da shi kan mukaminsa, kara masa girma da kuma biyan sa dukkan hakkokinsa a hukuncin da ta yanke mai lamba CA/A/248/2014, ranar 11/07/2014.

“A wannan lokacin Dikko Inde ne Shugaban Kwastam, sun dawo da ni aiki a matsayin mai kwangila na watanni shida ba cikakken ma’aikaci ba, kamar yadda kotu ta bayar da umurni, kuma ba su biya ni hakkokina ba. Bayan na yi korfi a kan haka, sai suka janye wasikar dawo da ni aikin da suka yi, duk da kuwa har an tura ni ofishin Hukumar da ke Garki Abuja da kuma Yaba Lagos a matsayin jami’i mai kula da lissafi. Watanni biyu kawai suka biya ni na Janairu da Fabarairu, 2015, daga nan suka dakatar har yau”, ya ce.

Gusau ya sake garzayawa Kotun Koli inda ya kai kukansa a kan take masa hakki da aka yi, ita ma ta yanke hukuncin a dawo da shi kan aikinsa, kuma a ci gaba da biyan sa hakkokinsa ranar 07/04/2017, “amma tun wancan lokacin Shugaban Hukumar Kwastam, Hamid Ali bai bi wannan umurnin ba,” in ji shi.

Ya ce duk hanyoyin da suka kamata ya bi don ganin an aiwatar da umurnin kotun, ciki kuwa har rubuta wasika zuwa Hamidi Ali a lokata daban-daban da Minista kudi Kemi Adeosun da Ministan Shari’a, Abubakar Malami, amma bai yi hakan ba.

Bello ya ce Lauyansa ma Gbenga Afolabi ya rubuta wasika ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Ministan Shari’a da Ministan Kudi da kuma Alkalin Alkalai na Tarayya, Hukumar Kwastam, Ma’aikatar Shari’a da sauran Hukumomi don a aiwatar da wannan umurnin na Kotun Koli, hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

A martanin da ta mayar kan wannan batu lokacin da manema labarai suka tuntube ta, Hukumar Kwastam ta kasa, ta hannun Jami’inta na hulda da jama’a, Joseph Attah, ta yi watsi da zarge-zargen.

Atta ya ce shi dai a iya saninsa, kotu ta lissafa wasu hakkokin Bello Gusau ne da yake korafin sun makale da suka hada da alwasu-alawus da kuma diyya, shi ne ta bayar da umurnin a biya masa su, kuma tuni sun bi wannan umurnin kamar yadda kotu ta bayar.


Advertisement
Click to comment

labarai