Connect with us

LABARAI

Martanin Gwamnati Ga Obasanjo: Mai Laifi Ne Kadai Ke Tsoron Bincike

Published

on


Gwamnatin tarayya ta bayyan rudewar da tsohon shugab kasa Olusegun Obasanjo ya yi bisa zargin cewa gwamnati na shirin kama shi da kulle shi har illa masha’allahu da cewa alama ce ta rashin gaskiya.

Ministan watsa labarai, Lai Mohammed, ne ya bayyana haka a wani sako daga mai bas hi shawara na musamman, Segun Adeyemi, a jiya Juma’a inda ya ce duk wanda bas hi da gaskiya kullum zai kasance cikin tsoro, hattana inuwarsa na iya tsora ta shi   take yi, domin kuwa wanda yake da gaskiya don ya ji an ce za a bincike shi hankalinsa ba zai tashi ba.

Ministan ya ci gaba da cewa, taratsi da za a yi ba zai kawar da hankalin gwamanati ba kan yin abin da  ya kamata ta yi, don gano dukiyar al’ummar da wadu suka yi rub-da-ciki a akanta

Ya ce yanzu abin da gwamanati ta sa agaba shi ne gyare-gyare a kan barnar da aka yi wa kasar nan ta shekara goma 16 ta tabbatar da cewa an dora kasar a kan hanya mai kyau.


Advertisement
Click to comment

labarai