Connect with us

LABARAI

Majalisar Dokokin Jihar Kano Za Ta ‘Yanta  Fursunoni 100

Published

on


Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa wani kwamiti karkashin Mataimakin Muhutin Majalisar Bala Yunusa wanda aka dorawa alhakin zakulo  daurarru 100 wadanda aka daure bisa kananan laifuka a gidanjen yarin Jihar Kano.   Alhaji Bala Yunusa  ne ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci ‘yan Kwamitin inda suka ziyarci Kwanturolan gidajen yarin Jihar Kano  Alhaji Magaji Ahmad a gidan yarin Kurmawa da ke Jihar Kano.

Shugaban Kwamitin ya shaidawa kwanturolan cewa wannan wani bangare ne na harkokin jinkai na ‘yan Majalisar dokokin Jihar Kano  domin tallafawa daurarrun, ya kara da cewa ‘yan majalisar sun damu kwarai da cinkoson   da ake fama dashi a gidajen yarin Jihar Kano dama Kasa baki daya.  Mataimakin muhutin Majalisar dokokin na JIhar Kano  yace wannan tallafin zai taimaka wajen rage cinkoso a gidajen yari da kuma sake hada daurarrun da iyalansu. Saboda haka sai ya bayyana aniyar Majalisar dokokin Jihar Kanon karkashin Jagoranci  Kakakin majalisar Honarabul Yusif Abdullahi Ata tabbacin kishin al’ummar Jihar Kano .

Da yake mayar da Jawabin Kwanturolan Gidajen Yarin na Jihar Kano  ya bayyana farin cikinsa bisa wannan ziyara, ya ci gaba da cewa  akwai  Matsalolin masu yawa  wanda suke haifar da cinkoson da ake fama dashi a Gidajen yarin, yace babbar matsalar itace ta shaye shayen miyagun kwayoyi.  Saboda haka sai kwantutolan ya bukaci gwamnatin Jihar Kano da ta yi kokarin samarwa da dandazon matasan Jihar Kano gurabun ayyukan yi domin samar da ingantacciyar al’umma.


Advertisement
Click to comment

labarai