Connect with us

LABARAI

Kashi 30 Zuwa 40 Na ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Tavin Hankaili—Masana

Published

on


Shugaban shirin kiwon lafiya da ake kira Mandate Health Empowerment Initiative, Mista  Zion Abba Ameh ya sanar da cewar,  ‘ yan Nijeria daga kashi 30 zuwa 40 bisa dari sun fama da tavin hankili.

Mista  Zion Abba ya bayyana hakan ne a cikin kasidar da ya gabatar a taron ya shafi lafiyar kwakwalwa da aka gudanar a Abuja.

Shugaban wanda ya yi amfani da alkaluman hukumar lafiya ta duniya (WHO) wajen fadar hujjar sa aka hakan yace, rahoton ya kuma bayyana cewar, mutane daga tsakanin kashi  16 zuwa kashi 49 a duniya suna dauke da alamun tavin hankali.

Acewar Mista  Zion Abba, ma fi yawancin wadanda suka fi fuskantar matsalar alumomin da ke zaune  kasashe masu katancin arziki ne.

Mista Zion Abba ya kuma  bayar da shawara da a sanya kudurin lafiyar kwakwalwa ta zama doka , ganin cewar dokar tavin hankali ta shekarar 1954 ba ta wani aiki a yanzu.

Ya kuma danganata shan kayan maye a matsayin daya daga cikin illolin da ke shafar lafiyar kwakwalwa, ya kara da cewa, idan muka yi magana a kan lafiyar kwakwalwa, muna nufin kwakwalwa, wadda ita ce mutum.

Shi ma a na sa jawabin, babban sakataren hukumar lafiya matakin farko Dakta Matthew Ashikeni ya yi nuni da cewar, nuna halin ko in kula da ake yi akan kiwon lafiyar kwakwalwa, inda hakan ya janyo kara hauhawar matsalar a kasar nan.

Acewar sa, kuma ba’a yi wani kokari ba wajen bayar da kwarin gwiwa a kan zuwa duba lafiyar ciwon kwakwalwa ba a mataki na farko kuma akwai bukatar a gwamnati ta gina asibiti na musamman don duba lafiyar kwakwalwa jama’a.

 


Advertisement
Click to comment

labarai