Connect with us

LABARAI

Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan 1.1 A Watan Mayu

Published

on


Hukumar kwastam, ta sami nasarar tara tsabar kudi Naira biliyan 1.1, a watan Mayu, wanda haka ya kafa tarihin da ba a taba cim ma ba a hukumar. Kan hakan kuma sai hukumar ta nemi da a yi wa ma’aikatanta karin albashi.

Babban Kwanturolan hukumar na kasa, Hameed Ali, ne ya bayyana wannan nasarar da hukumar na su ta samu, ya kuma hada da bukatar tasu ta neman a yi masu karin albashi, a lokacin da hukumar ke gudanar da bukin yaye wasu manyan ma’aikatanta su 40, bayan da suka kammala wani kwas na watanni biyar a kwalejin ma’aikatan hukumar da ke Gwagwalada, Abuja, shkaran jiya.

Ya nemi da a yi wa zaratan hukumar na shi karin albashi, inda ya kara da cewa, “Tare da wannan namijin kokarin da muke na tara wa gwamnati kudade, muna rokon da a duba albashinmu da nufin yi mana kari.

Ya kuma umurci daliban da suka sauke karatun nasu da su yi aiki da abin da suka karanta, ya kuma nemi gwamnati da ta kara martaba Kwalejin ta su. Ya ce, “Kwatankwacin makarantu irin wannan na Sojoji, kai tsaye suka amsan kasafin kudadensu daga Majalisa. Muna fatan hukumar kula da aikin kwastam za ta yi mana wani kokari a kan hakan.

Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, wanda ya mika takardun kammala karatu ga wadanda aka yayen, ya nuna mahimmancin samar da irin wannan kwasa-kwasan ga hukumomi.

Osinbajo, wanda ya aminta da shawarar ta Hameed Ali, na neman a yi wa ma’aikatan hukumar ta kwastam karin albashi bisa la’akari da namijin kokarin da suke yi na tara kudade, ya ce, hukumar ta kwastam, ta tara Naira triliyon 1.3 a shekarar 2017, abin da ba a taba tara kamarsa ba a tarihin hukumar.

Ministar kudi, Adeosun, wacce daraktan ma’aikatar ta kudi, Uwargida Olubunmi Siyanbola, ta wakilce ta, ta nemi hukumomin na hukumar kwastam ne da su kara kaimi wajen horas da ma’aikatan su, ta kuma tabbatar masu da samun hadin kan ma’aikatar nata.


Advertisement
Click to comment

labarai