Connect with us

LABARAI

Fashi Da Makamin Offa: ’Yan Sanda Na Kara Tattara Hujjoji A Kan Saraki

Published

on


A jiya ne rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta fitar da sanarwar cewa tana kara tattaro hujjoji daga ‘yan fashin Offa wadanda ke nuna dumu-dumu akwai hannun Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.

A ta bakin ‘yan sandan, karin hujjar da suka samu ta hada da hoton daya daga cikin ‘yan fashin yayin da ya ziyarci daurin auren diyar Saraki.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana wannan hujja a matsayin wata babbar shaidar da suka samu akan Shugaban Majalisar na Dattawa wanda ke a alakanta shi da harin ta’addanci na fashi da makami da aka kashe mutum 33 a garin Offa.

Takardar ta bayyana cewa; “ Wasu karin bayanai na hujjoji sun tabbatar mana da cewa, dukkanin shugabannin da suka jagoranci harin fashi da makamin Offa; Ayoade Akinnibosun, Ibukunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salawudeen Azeez, Niyi Ogundiran suna da alaka da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki.

“Mutum biyar din da suka jagoranci wannan fashi da makami sun halarci bukin daurin auren diyar Saraki wanda ya gudana a kwanakin baya.” Inji Kakakin rundunar ‘yan sandan Nijeriya, Jimoh Moshood.

Idan dai ba a manta ba, da farko rundunar ‘yan sandan ta bukaci Saraki ne da ya bayyana a gabanta don ya amsa tambayoyi dangane da harin Offa, inda kuma daga bisani ta bayyana cewa, ba sai ya bayyana ba, yana iya rubuto jawabinsa a rubuce. Inda rundunar ‘yan s

andan ta ba shi awowi 48 da ya kammala rubuta jawabin nasa.

Sai dai wannan sabon ikirari na ‘yan sanda ya fito ne kwana guda da gamayyar ‘yan majalisu suka fitar da sharudda 12 wanda a cikinsu suke so gwamnatin Buhari ta tabbatar da ta yi aiki da guda 10.


Advertisement
Click to comment

labarai