Connect with us

LABARAI

An Kira Ga Gwamnatoci Da Su Fito A Dama Da Su A Harkokin Noman Rani A Jihar Yobe

Published

on


Mai bada shawara kan harkokin tattalin arziki ga gwamna Alhaji Ibrahim

Gaidam na Jihar Yobe Alhaji Madu Aji Juluri ya kirayi daidaikun gwamnatocin da ake da su, da su ci gaba da

tallafawa kan harkokin noman rani a Jihar Yobe.

Alhaji Madu Aji ya yi wannan kira ne a tattaunawarsa da wakilin mu agarin Damaturu.

Ya kara da cewar kasancewar noman rani na daga cikin hanyar habaka tattalin arzikin al’ummomin dake gudanar da shi musamman anan Jihar ya

zama abin bukata da a kawo dauki ga masu gudanar da shi.

Alhaji Madu juluri ya ci gaba da cewar, manoman rani a bara sun samu

amfanin gona mai tarin yawa musamman manoman garuruwan Kaliyari da

Juluri duka a karamar hukumar Bursari amma kuma duk haka ambaliyar ruwan da yankin ya yi fama da shi a shekarar ta bara ya lalata gonake kusan 50 dauke da amfanin gona mai tarin yawa.

A cewarsa, a halin da ake ciki matukar matasa sun gano muhimmancin da noman rani ke da shi kan ciyar da tattalin arzikin kasa gaba da kawar da zaman kashe wando musamman a yankin arewa maso gabas.

Ya ci gaba da cewa kasar mu Nijeriya Allah ya arzurtata da kasa mai yalwa wadda duk abin da aka shuka matukar an kula da shi to kuwa akan samu amfanin gona mai tarin yawan gaske.

Alhaji Madu ya kuma yabawa gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam na Jihar Yobe dangane da yadda ya ke daukar matakan da suka dace na ciyar da harkokin aikin gona gaba ta kowane bangare musamman harkokin noman rani a dukanin fadin Jihar ta Yobe duba da yadda mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ke daukar harkokin noma da muhimmanci a kasar nan.


Advertisement
Click to comment

labarai