Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Bilyan Daya Kan Inganta Kwalejin Kimiyya Ta Bauchi – Gumau

Published

on


Gwamnatin Tarayya a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ta kaddamar da ayyuka daban-daban wanda yawan kudinsu ya kai kimanin kusan naira Biliyan guda a kwalejin kimiyya, fasaha da kuma kere-kere mallakinta da ke Bauchi daga lokacin da gwamnatinsa ta hau karagar mulki.

Ayyukan da Buhari ya samu gudanarwa sun hada da samar da manya-manyan dakunan karatu, hanyoyin da zai saukake zirga-zirga a cikin kwalejin hade da gina sassan tsangayar koyar da ilimi guda hudu da sauran ayyukan raya kwalejin.

Da yake zantawa da manema labaru, shugaban Kwalejin Sanusi Gumau ya shaida cewar kashi 90 cikin 100 na ayyukan ya samu tallafin ne daga asusun tallafa wa manya-manyan makarantu wato ‘Tetfun’.

Sunusi Gumau ya bayyana cewar sabbin sassan da aka gina su a karkashin gwamnatin Buhari sun hada da sashen koyar da aikin jarida, sashin dakin nazarin ilimin kimiya, sashin koyar da kiwon kifi, hade da samar da sashin koyar da na’ura mai kwakwalwa wato Computer da kuma samar da tsangayar koyar da harkar gona na zamani.

Ta bakinsa; “Abun da na ke fada in ka zaga cikin makarantar za ka ga ana gine-gine, wadannan sabbin gine-ginen nan da kuma abubuwan da aka sayo an yi ne domin inganta karatu tun daga kan koyo da kuma koyarwa.

“Ayyukan idan ka kiyasce za su kai kudi naira miliyan dari tara da dauriya,” In ji shugaban kwalejin.

A fannin ma’aikata kuwa, ya bayyana cewar a kwana-kwanan nan Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya amince da basu dukkanin alawus-alawus din malaman da suke bi, hade da tabbatar da bada tallafin kudaden da ake bayarwa na wata-wata ba tare da bata wani lokaci ba.

Haka nan, ya kara da cewa akwai malamai da daman gaske da aka dauki nauyin karo karatunsu a jami’o’in da suke cikin kasa da wajenta “A yanzu yau din nan da na ke maka magana (ranar da aka tattauna da shi) ma’aikatanmu guda uku daga cikinsu sun tafi jihar Sokoto domin su gano mene ne ke tafiya a can don muna son mu kawo wani tsarin da zai bamu zarafin rage dogaro da karfin wutar lantarki ta NEPA,” In ji Gumau.

Sanusi Gumau ya yaba wa kokarin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a bisa irin wannan namijin kokarin da yake yi wajen ciyar da sha’anin ilimi a kowace gaba, yana mai shan alwashin yin duk mai yiwuwa wajen kula da ababen da gwamnatin tarayyar ta samar a kwalejin ta yadda ‘ya’yan baya ma za su mora.


Advertisement
Click to comment

labarai