Connect with us

LABARAI

Gidauniyar Tallafa Wa Ilimi Ta Wayar Da Kan Yaran Arewa

Published

on


kungiyar tallafawa ilmin kananan yara (Children Education Support Eniciatibe) wadda daga Arewacin Nijeriya ta ke ta shirya taro na musamman ga yara domin ba da tata gudunmawar ga bangaren ilmi.

Kungiyar ta gudanar da taron na bana ne a ranar 27 ga watan Mayu wanda ranar ce ake yin bikin ranar yara ta duniya. Idan dai ba manatawa aka yi ba, majalisar dinkin duniya ita ce ta ware ranar duk shekara saboda a rika mutunta su ma yara da kuma kulawa da su.

Cikin ikon Allah sai gashi a wannan shekarar gidauniyar taimakawa kananan  yara daga Arewacin Nijeriya, ita ma ta bi sahun gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kansu domin nunawa yara suma su san cewar ba mantawa aka yi dasu ba, su ma suna da rawar da za su iya takawa nan gaba.

Gidauniyar ta gaiyato yara daga shiyyoyi uku na Arewa wadanda suka hada da Arewa maso yamma, Arewa ta tsakiya, da kuma Arewa maso gabas, shugaban ita gidauniyar na kasa Komrade Sa’idu Sambo ya bayyanawa manema labarai cewar an gaiyato su ne daga ko wanne sako da kuma lungu na Arewacin kasar nan saboda a  fadakar dasu akan muhimmancin ilmi duk da yake a matsayinsu na yara, sun san dalilin da yasa Iyayensu suka sa su a makaranta, bugu da kari  shi kan shi shugaban gidauniyar ya samu  kan shi ya bar makaranta, ba tare da ya samu wani ilmi mai zurfi ba. Wannan dalili ne ya sa shi ma ya kara sa kaimi da kuma himma wajen shima irin gudunmawar da zai bada akan ilmin yara kanana.

Manayan bakin da suka halarci wannan gaggarumin taro sun hada da shugaban Karamar Hukumar babban birnin tarayya Abuja Honorabul Abdullahi Adamu Candido, wanda Baban Goshi ya wakilce shi, da kuma Sanata Wowo wanda shi ma ya samu wakilci ne na sarakunan gargajiya da kuma sauran manyan baki.

Yara su ne manyan gobe ashe kuwa ya kamata ke nan a basu kyakkyawar kulawa wajen tarbiyartar da su su tashi wadanda ake sha’awar halayensu, ita kanta tarbiyyar cikin ilmi ake koya ma su yara nau’i nau’i na ita tarbiyar.

 


Advertisement
Click to comment

labarai