Connect with us

LABARAI

Bajamushe Ya Tona Yadda A Ka Damfare Shi Dala 55,00 A Nijeriya

Published

on


Wani dan kasar Jamus mai sayar da motoci mai suna Mista Michael Kramer ya shaida wa kotun da ke sauraron kararraki na musamman da ke  Ikeja a cikin jihar Legas cewar, sanannen mutumin da ake zargin dan damfara ne Fred Ajudua ya damfare shi dala  550,000 a cikin shekaru ashirin da biyar da suka wuce.

wanda ya bayya shedawa Kotun hakan ne a ranar talatar data gabata.

Mista Michael Kramer ya yi zargin cewa Ajudua da abokin sa Joseph Ochunor suka hadu suka yi ma sa wannan ta’asar. Mutanen biyu dai suna fuskantar tuhuma sha biyu kuma an gurfanar da su ne a gaban Alkalin Kotun mai shari’a Mojisola Dada.

Mista Michael Kramer  ya fada wa kotun cewar sakamakon damfarar, ya yi asarar gidan sa da kasuwancin sa kuma matar sa ta gudu saboda ba zai iya ci gaba da  kula da ita da kuma ‘ya’yan da suka haifa ba.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai